‘Yansandan jahar Kano Sun Ceto Yaro Ɗanshekara 2 daga hannun masu garkuwa da mutane, Sun kuma Kama Mutum Uku tare da Kwato Naira 930,000 na Kuɗin Fansa.
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasarar ceto wani yaro ɗanshekara 2 da aka yi garkuwa da shi ba tare da ya samu wani rauni ba, tare da kama mutane uku (03) da ake zargi, da kuma kwato wani ɓangare na kuɗin fansa da aka biya, sakamakon wani aiki na sirri da aka gudanar cikin tsari.
A ranar 19 ga Afrilu, 2026, wani mazaunin Unguwar Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala ya kai rahoton cewa an yi garkuwa da ɗansa, Aliyu Aliyu Muhammad (namiji), mai shekaru 2, a gaban gidansu ta hannun wasu da ba a san ko su wanene ba.
Bayan haka, masu garkuwar sun tuntuɓi iyalan yaron inda suka nemi kuɗin fansa na Naira miliyan ɗaya (₦1,000,000.00), wanda iyalan suka biya. Duk da karɓar kuɗin, ba su saki yaron ba.
Da samun rahoton, Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, sfipma, mnim, mnips, masis, ya ba Rundunar Yaƙi da Garkuwa da Mutane umarni da su yi amfani da dukkan dabarun aiki da na sirri domin gano masu laifin. Ta hanyar bin diddigi da amfani da fasahar zamani, an gano maboyar su tare da kama su.
Waɗanda aka kama sun haɗa da:
i. Hassan Umar, namiji, mai shekaru 26,
ii. Abdullahi Hamisu, namiji, mai shekaru 19, da
iii. Hussaini Saminu, namiji, mai shekaru 24, dukkaninsu mazauna Unguwar Gwammaja a Kano.
Bincike ya nuna cewa an tsare yaron a gidan Hussaini Saminu da ke cikin Unguwar Gwammaja. An ceto shi lafiya ba tare da wata illa ba, kuma an mayar da shi ga iyalansa.
Haka kuma, an kwato jimillar Naira 930,000 daga cikin kuɗin fansa daga hannun waɗanda ake zargin.
Kwamishinan ‘Yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewa, ƙwarewa da kuma ingantaccen aiki na Rundunar Yaƙi da Garkuwa da Mutane wajen ceton yaron lafiya. Ya kuma gode da jagorancin fasaha daga ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, psc(+), NPM, wanda ya taimaka matuƙa wajen samun nasarar wannan aiki. Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka ba tare da gajiyawa ba.
CP Bakori ya gargaɗi masu aikata laifuka cewa Jihar Kano za ta ci gaba da zama wurin da ba shi da aminci gare su, domin rundunar za ta yi amfani da dukkan hanyoyin doka wajen kamo su da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da su riƙa sanya ido sosai kan yaransu, tare da sanar da duk wani motsi ko aiki mai tayar da hankali ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Ya kuma ƙarfafa guiwar jama’a da su ci gaba da bai wa ‘yansanda haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai ta layukan gaggawa na rundunar: 08032419754, 08123821575 ko 09029292926.
Bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Domin ƙarin bayani ko talla ko labarai, za ku iya kiranmu ta kan wannan lambar wayar 08036614747
