Featured News

KUNGIYAR NUT TA GWALE TARE DA KUNGIYAR MALAMAI MATA SUN KAI WA MALAMA NAFISA ABDULLAHI TALLAFIN KUƊI NA KIMANIN ₦405,000

IMG 20251207 WA0001
IMG 20251207 WA0001

Kungiyar Malaman makaranta ta NUT reshen karamar hukumar Gwale tare da kungiyar Malamai mata da AOPSHON da kungiyar SUPA sun kai wa Malama Nafisa Abdullahi gudummawar kuɗin da za a yi mata aiki a asibiti a matsayinta ta ɗaya daga cikin Head Teachers ta karamar hukumar Gwale LGEA.

IMG 20251207 WA0014
NUT GAYA

Shugaban ƙungiyar NUT ta Gwale Comrade Sani Rabiu Dandago ne ya ja tawagar kai tallafin kuɗaɗen nema wa Malama Nafisa Abdullahi lafiya akan jiyyar da ta ke yi wanda kuɗin ya tasamma sama da Naira miliyan ɗaya da ɗoriya. Comrade Ɗandago ya bayyana wa manema labarai ce wa, ita fa wannan baiwar Allah mara lafiya ta jima tana fama da wannan jiyya wadda ake neman sama da miliyan ɗaya domin yi mata wasu allurai da magungunan da za ta ke sha . Wannan hakan ne ya sa abokan aiki da kuma ita kanta kungiyar NUT ta Gwale su ka yanke shawarar nema mata taimako a tsakanin malaman makaranta na karamar hukumar Gwale. Wanda a wannan rana ta Asabar 6/12/2025 ne aka taso tare da wasu malamai daga ɓangaren NUT da kuma na kungiyar malamai mata domin kawo mata wannan tallafin kuɗaɗen da aka tara kimanin Naira dubu ɗari huɗu da biyar (₦405,000) , domin a haɗa da su wajan saya mata magunguna.

Comrade Ɗandago ya ƙara da ce wa, a yanzu kafin su taho an samu wasu ma sun tura nasu kuɗin. Wanda hakan na nuna ce wa, za a sake kawo mata kuɗin da aka sake tarawa a lokaci me zuwa. Dandago ya yaba wa dukkannin malaman da su ka bada gudummawarsu tare da fatan Allah ya saka wa kowa da Alkhairi.

Baba Comrade, E-Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *