Tsohon Ma’aikaci Sani Adamu Kofar Naisa Ya Jinjinawa Gwamna Abba Yusuf Bayan Karɓar Kuɗin Gratuity da Ya Dade Yana Jira
“Ina matuƙar godiya ga Gwamna Abba—Alhamdulillahi, na samu kuɗina na gratuity.”
Malam Sani Adamu Kofar Naisa, wanda a baya kafafen yaɗa labarai suka bayyana matsalarsa tare da kai kukansa ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan kuɗin gratuity ɗinsa da suka makale tsawon shekaru takwas, ya bayyana matuƙar godiya bayan da aka biya shi haƙƙinsa.
Ya miƙa sakon godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kuma kafafen yaɗa labarai da suka taimaka wajen isar da kukansa, musamman Premier Radio, E-Magazine Media Channel Production, da Community Pen.
Comrade Sani Adamu ya bayyana matuƙar farin cikinsa bayan samun saƙon shigar kuɗi (credit alert) a asusunsa, wanda ya tabbatar da biyan gratuity ɗinsa. Wanda hakan ne ya sa ya yi wa gwamnan addu’a, a inda ya yi roƙo ga Allah da ya ba shi nasarar sake komawa kan mulki tare da kare shi daga sharrin maƙiya. Haka kuma, ya yi addu’a ga mahaifiyar Gwamnan, yana roƙon Allah ya ƙara mata lafiya da tsawon rai.
