News

Tsofaffin ‘Yan Jarida sun nuna goyon bayansu ga tsarin kundin Ƙa’idojin Ƙungiyar tsofaffin ‘Yan Jarida na jahar Kano

2dc5357d f704 4eec 8293 e0d1f639e01e 1068x707 1 768x508
2dc5357d f704 4eec 8293 e0d1f639e01e 1068×707 1 768×508

Tsofaffin ‘Yan Jarida sun nuna goyon bayansu ga tsarin kundin Ƙa’idojin Ƙungiyar tsofaffin ‘Yan Jarida na jahar Kano

Yanƙungiyar tsofaffin ‘Yanjarida na jahar Kano (KALVEJ) sun amince da ake amfani da kundin ƙungiyar a hukumance, a wani taro da aka gudanar a ranar Laraba.

Ƙungiyar ta yi wani zama ne da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) da Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano, domin tallafa wa matasan ‘yan jarida domin ƙarfafa musu guiwa wajan bin ƙa’idojin aiki, da kuma kiyaye tarihin aikin jarida a jahar Kano.

images (9)

A watan Augusta 2025 ne aka kafa kwamitin da zai tsara tsarin ƙungiyar, inda aka duba daftarin kundin ƙa’idar ƙungiyar a ƙarshen shekarar 2025, wani mataki na ci gaba wajen kaddamar da ita a matsayin jagora ga aikin jarida a Kano.

Taron wanda wani hadimin Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Malam Auwalu Mu’azu ya tsara a Tahir Guest Palace. A taron an tattauna akan abubuwa da dama tare da yin  sharhi da nazari daga mambobin NUJ da suka fito daga fannoni daban-daban na aikin jarida, ciki har da masana daga jami’o’i.

Daga cikin abubuwan da aka lura da su a cikin kundin, wanda yanzu ya zama tsarin mulkin ƙungiyar, akwai rashin tanadin jin daɗin mambobi, wakilcin jinsi da tsarin samun kuɗi na gudanarwa.

Bayan dogon nazari, an yanke shawarar tura waɗannan batutuwa zuwa ga Kwamitin rubuta Kundin tsari domin sake duba su.

A jawabin sa, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jahar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa, ƙungiyar ba reshe ba ce na Ma’aikatar Labarai, kuma tana aiki ne a matsayin ƙungiya mai zaman kanta tare da dangantaka ta sana’a ga ma’aikatar.

A ƙarshen taron, an yanke shawarar bai wa Kwamitin rubuta kundin tsarin damar ci gaba da tafiyar da harkokin ƙungiyar har na tsawon shekara guda, kafin a gudanar da zaɓen shugabanni na dindindin.

Shugaban kwamitin, Alhaji Ahmed Aminu, ya gode wa mahalarta taron bisa amincewar da suka yi tare da alƙawarin cewa, za a gyara kundin domin haɗa bukatun jin daɗin mambobin ƙungiyar da sauran batutuwan da aka bayyana.

Baba Comrade, E-Magazine

7/1/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *