SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR GWALE YA ƘADDAMAR DA RABON BAWA SABBIN MALAMAN MAKARANTA TAKARDAR KAMA AIKI SU 505, ZA A BASU ALBASHIN JULY 2026
A wani muhimmin mataki na ci gaba da inganta harkar ilimi a Ƙaramar Hukumar Gwale, Mai Girma Zababben Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Hon Abubakar Ma’azu Mojo, a yau Litinin ya jagoranci bikin ƙaddamar da rabon Takardun Kama Aiki (Teaching Offer) ga sababbin malamai 505 da Gwamnatin Ƙaramar Hukumar Gwale ta ɗauka aiki bisa sahalewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf. An gudanar da bikin ne a harabar Sakatariyar Mulki ta Ƙaramar Hukumar Gwale.
Wannan shi ne kaso na uku na ɗaukar malamai da gwamnatin Ƙaramar Hukumar Gwale ta aiwatar tun bayan hawanta mulki, inda ya zuwa yanzu aka ɗauki kusan malamai 2,000, a wani gagarumin shiri na ƙarfafa ilimin yara da magance ƙarancin malamai a makarantun firamare na ƙaramar hukumar.
A jawabinsa yayin taron, Mai Girma Hon. Abubakar Mu’azu Mojo ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ba ilimi fifiko domin tabbatar da cewa ɗaliban Gwale sun samu ingantaccen ilimi a hannun ƙwararrun malamai. Ya kuma buƙaci sababbin ma’aikatan da su kasance masu kishin aiki, gaskiya da riƙon amana wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Shi ma a nasa jawabin, Education Secretary na Ƙaramar Hukumar Gwale Malam Muktar Inuwa ya taya sababbin malaman murna tare da yi musu albishir cewa Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar, Hon. Abubakar Mu’azu Mojo, zai bayar da umarni nan take domin a saka sunayensu cikin tsarin biyan albashi, ta yadda za su fara karɓar haƙƙoƙinsu cikin gaggawa, a wani mataki da ke nuna jajircewar gwamnatin wajen kula da walwalar ma’aikatanta da cika alƙawuran da ta ɗauka.
An kammala taron cikin farin ciki da addu’o’in fatan alheri ga gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf da kuma gwamnatin Ƙaramar Hukumar Gwale ƙarƙashin jagorancin Hon. Abubakar Mu’azu Mojo, bisa ci gaba da aiwatar da manufofin bunƙasa ilimi da inganta rayuwar al’ummar Gwale
