Rikicin Siyasa: Nafi’u Roja Ya Ajiye Shugabancin Majalisar Kumbotso, An Zabi Sabon Shugaba
Shugaban Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Nafi’u Roja, ya ajiye mukaminsa na shugabanci bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan rabuwar Gwamnan Jihar Kano da jagoran siyasa Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya biyo bayan zaman majalisar da aka gudanar domin warware takaddamar shugabanci da ta dabaibaye majalisar a ‘yan kwanakin nan.
Sanarwar da Ofishin Daraktan Mulkin Karamar Hukumar Kumbotso ya fitar a ranar Talata ta tabbatar da cewa bangarorin da ke takaddama kan shugabanci sun cimma matsaya ta sulhu domin tabbatar da hadin kai da kuma ci gaban majalisar.
A cewar sanarwar, Hon. Nafi’u Roja ya rubuta takardar ajiye mukaminsa cikin lumana, domin bai wa zaman lafiya da hadin kai damar tabbata a majalisar.
Bayan haka ne kansiloli tara cikin goma sha daya suka gudanar da sabon zabe, inda suka zabi Hon. Isyaku Idris, kansilan mazabar Kumbotso kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar, a matsayin sabon Shugaban Majalisar Kansiloli.
Haka kuma, an zabi Hon. Shehu Danyaro, kansilan mazabar Na’ibawa, a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.
Tun da farko dai rikicin shugabancin majalisar ya kai har ga shigar da kara a kotu kan sahihancin cire tsohon shugaban. Sai dai sabon ci gaban ya nuna cewa an kawo karshen takaddamar ta hanyar sulhu, lamarin da ake sa ran zai dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a majalisar.
Idan kuna son a yi muku talla ko wallafa labarai ku neme mu ta lambar waya
08036614747
