Uncategorized

MAJALISAR DOKOKIN KANO TA KI AMINCEWA DA YUNKURIN SAKA SANATA KWANKWASO CIKIN TAKUNKUMIN AMURKA

1771943821020
1771943821020

MAJALISAR DOKOKIN KANO TA KI AMINCEWA DA YUNKURIN SAKA SANATA KWANKWASO CIKIN TAKUNKUMIN AMURKA

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana rashin amincewarta da wani kudirin doka da ake shirin gabatarwa a Majalisar Dokokin Amurka, wanda ya ambaci sunan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso cikin jerin mutanen da ka iya fuskantar takunkumi, ciki har da hana su biza da kuma dakatar da kadarori a kasar.

An bayyana wannan matsaya ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kiru, Hon. Usman Tasiu, ne ya gabatar da kudirin, inda ya bayyana Sanata Kwankwaso a matsayin jajirtaccen jagora wanda ya sadaukar da kansa wajen hidimtawa al’umma, tare da cewa jagorancinsa ya yi tasiri mai kyau ga rayuwar al’ummar Jihar Kano.

A cewarsa, tsohon gwamnan ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya, bunkasa harkokin ilimi, da samar da muhimman ayyukan more rayuwa ba tare da nuna bambanci tsakanin addinai ko kabilu ba. Ya kara da cewa Sanata Kwankwaso ya dade yana kokarin hada kan al’umma tare da nuna adawa da duk wani nau’i na tashin hankali ko musgunawa jama’a.

Bayan tattaunawa, majalisar ta amince da kudirin tare da yin kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta dauki matakan gaggawa da suka dace domin mayar da martani kan shirin dokar.

A wani bangare na zaman, majalisar ta kuma amince da wasu kudurori da suka shafi gina hanyoyi a kananan hukumomin Tarauni, Madobi da Garun Malam.

Kudurorin sun samu goyon baya daga ‘yan majalisa da suka hada da Kabiru Dahiru (Tarauni), Sulaiman Ishaq (Madobi), Mataimakin Kakakin Majalisa Muhammad Bello, da Zakariyya Alhassan (Kura/Garun Malam), inda suka jaddada bukatar bunkasa ababen more rayuwa domin saukaka zirga-zirga da habaka tattalin arzikin yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *