ƘUNGIYAR NUT TA KAIWA MALAM UBALE ADO DAUKIN GAGGAWA
Ƙungiyar Malaman makaranta ta Nigeria (NUT) reshen karamar hukumar Nassarawa ta kai wa malam Ubale Ado tallafin kuɗi a ranar Juma’a 30/1/2026 bisa iftila’in gobara da ta babbake masa gidansa.

Shugaban ƙungiyar Comrade Nura Lawal tare da wasu jagororin kungiyar ne su ka mika wannan tallafi na ₦70,000 tare da jajanta masa . Lawal ya ƙara da cewa, iftila’in da ya samu malam Ubale Ado abun a tausaya masa ne, duba da yadda wutar ta babbake masa gidansa kusan gaba ɗaya .
Ubale Ado na ɗaya daga cikin ma’aikatan Nassarawa LGEA wanda ya ke aiki a sashen adana takardu(Registry).
Malam Ado ya yi godiya ga NUT bisa wannan tallafi da su ka kawo masa har gida.
Baba Comrade, E-magazine
30/1/2026
