NUT KANO TA YI KIRA GA MALAMAN MAKARANTA DA SU ƘAURACE WA JITAJITA DA BATANCI GA ƘUNGIYAR
Kungiyar malaman makaranta,Nigeria Union of Teachers (NUT) reshen Jihar Kano tana sanar da dukkan malamai, musamman malaman firamare da sakandare, cewa tana bakin ƙoƙarinta matuƙa wajen kare muradunsu, haƙƙoƙinsu da walwalarsu a kowanne lokaci. Batun ƙarin albashi, inganta walwala, da tabbatar da mutuncin malamai ba wai magana ce ta yau da gobe ba, lamari ne da muke bibiyarsa tuntuni har zuwa yanzu ba tare da gajiyawa ba.
Muna sane da halin ƙuncin rayuwa da malamai ke ciki, da yadda hauhawar farashi ke shafar kowa, musamman ma ma’aikatan ilimi. Saboda haka, muna so malamai su fahimci cewa duk yadda muke da ƙwazo da niyyar ganin an gyara albashinsu, ba mu da ikon ƙara wa ma’aikata albashi da kanmu. Aikin ƙungiya anan shi ne tattaunawa, wakilci, matsin lamba ta hanyar doka, da isar da muradun malamai kai tsaye ga gwamnatin jiha da hukumomin da abin ya shafa. Kuma a kullum muna kan wannan magana, ba dare ba rana.
Abin takaici ne yadda wasu malamai, saboda rashin sanin irin ƙoƙarin da ake yi a bayan fage, suke ganin kamar ba a yin komai, har ma su kai ga yin zagi ko cin mutuncin shugabannin ƙungiya. Wannan ba adalci ba ne. Domin duk wanda ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a yanzu, zai fahimci cewa ƙungiyar NUT ba ta taɓa sakaci da haƙƙin malamai ba, kuma ba za ta yi shiru ba a duk lokacin da aka tauye su.
Idan muka duba batun promotion, wannan hujja ce ƙarara da ke nuna irin cigaban da aka samu. Tun bayan haɗin guiwar da aka ƙarfafa tsakanin Hukumar Ilimi da NUT, babu wata ma’aikata a wannan jiha da ta fi malamai samun promotion akan lokaci kamar yanzu. Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, an samu ci gaba mai ma’ana, kuma hakan ba zai yiwu ba sai da tsayuwa tsayin daka da kuma bibiya ta kusa da ƙungiya ke yi.
Haka zalika, ƙungiyar NUT tana ci gaba da bibiya kan gyaran albashin malaman firamare, da biyan basussuka, da duk wani abu da ya shafi jin daɗi, tsaro, da martabar malamai. Ba mu tsaya a magana kawai ba, mun kai ƙorafe-ƙorafe da shawarwari a rubuce kuma masu muhimmanci ga Gwamnatin Jahar Kano. Mu na roƙo da jan hankali kan abubuwan da ya kamata a yi domin inganta harkar ilimi.
Daga cikin muhimman buƙatun da muka miƙa wa gwamnatin jahar Kano sun haɗa da:
1- Neman Inganta albashin malamai bisa la’akari da halin da rayuwa ke ciki.
2- Biyan dukkan haƙƙoƙin malamai akan lokaci ba tare da jinkiri ba
3- Tabbatar da adalci da gaskiya a tsarin promotion
4- Samar da walwala da kariya ga malamai a wuraren aiki
5- Ɗaukar ilimi da malamai a matsayin ginshiƙin cigaban al’umma
Muna so mu jaddada cewa, duk wani cigaba da aka samu a yau ba wai ya zo da sauƙi ba ne. Ya zo ne sakamakon haƙuri, jajircewa da haɗin kai. Saboda haka, muna kira ga dukkan malamai da su ci gaba da nuna fahimta, su guji yanke hukunci cikin gaggawa, su kuma guji sauraron jita-jita daga waɗanda ba su da cikakken bayani.
A ƙarshe, ƙungiyar Nigeria Union of Teachers (NUT) Kano State Wing na tabbatar wa malamai cewa , ba za ta taɓa barin muradunsu a baya ba. Za mu ci gaba da tsayuwa tsayin daka wajen kare haƙƙinsu, har sai an cimma abin da ya dace. Muna kira ga malamai da su kasance tare da ƙungiyarsu, domin haɗin kai shi ne mabuɗin nasara, kuma da yardar Allah, sakamakon wannan ƙoƙari zai bayyana a fili nan gaba kaɗan.
🖊️ Najib Abdullahi musa , Garin Malam
