NNPP: MUN YABA DA YADDA INEC TA GUDANAR DA ZABEN CIKE GURBI NA MUNICIPAL DA UNGOGO
Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso reshen Jihar Kano ta yaba wa Hukumar INEC kan yadda aka gudanar da zaɓen cike gurbi cikin lumana a Kano.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran NNPP a Jihar Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya fitar a ranar Asabar 21 Fabrairu 2026.
Sanarwar ta ce jam’iyyar ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen, tare da taya murna ga ’yan takararta biyu da ta fara tsayarwa kafin daga baya ta janye sunayensu domin kauce wa matsalar kai suna sau biyu da ka iya jawo soke takara daga INEC.
Sanarwar ta ƙara da cewa jam’iyyar ta nuna damuwa kan ƙarancin fitowar masu zaɓe, inda ta danganta hakan da sauya sheƙar gwamnan zuwa APC, tare da cewa mafi yawan al’ummar Kano magoya baya ne na Kwankwasiyya.
