Education

Gwamnatin Kano ba ta da wani shirin yin musayar filin makarantar FGC Kano, a guji yaɗa jitajita

1775516803414
1775516803414

Gwamnatin Kano ba ta da wani shirin yin musayar filin makarantar FGC Kano, a guji yaɗa jitajita

Gwamnatin Jihar Kano ta ja hankalin al’umma gaba ɗaya kan wasu rahotanni da wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa dangane da zargin wata yarjejeniyar musayar fili da ake dangantawa da Kwalejin Tarayya ta Kano (FGC Kano).

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Litinin.

Gwamnatin ta bayyana a sarari cewa ba ta da hannu a kowanne irin tsari ko tattaunawa ko yarjejeniya da ta shafi wannan fili da ake magana a kai.

Ta ƙara da jaddada cewa Kwalejin Tarayya ta Kano na ƙarƙashin cikakken ikon Gwamnatin Tarayya ne ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wadda ita kaɗai ke da alhakin yanke duk wani hukunci da ya shafi makarantar.

Haka kuma, gwamnatin ta fayyace cewa duk wani yunƙuri na danganta gwamnatin Abba Kabir Yusuf ko wasu na kusa da shi da wannan zargin, ba shi da tushe kuma na yaudara ne.

Duk da amincewa da damuwar da jama’a suka nuna, gwamnatin ta bukaci kafafen yaɗa labarai da su kiyaye ƙa’idojin gaskiya, adalci da aikin jarida mai nagarta, tare da kaucewa wallafa rahotannin da ba a tantance ba ko na hasashe.

A ƙarshe, gwamnatin ta sake jaddada aniyarta na bin gaskiya, mutunta doka, da kuma kare muradun al’umma.

Sa hannu:

Mustapha Muhammad

Babban Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan Kano

Domin neman karin bayani ko isar da sako ko talla , a tuntube mu ta lambar waya 08036614747

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *