GWAMNA ABBA YA BAR JAM’IYYAR NNPP
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a hukumance, inda ya danganta hakan da tsanantar rikice-rikicen cikin gida da kuma bukatar kare muradun al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
A cikin wata wasika da ya aikawa Shugaban NNPP na mazabar Diso-Chiranchi, Karamar Hukumar Gwale, Gwamna Yusuf ya sanar da janyewarsa daga jam’iyyar tun daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.
“Ina rubuto wannan wasika ne cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a hukumance game da shawarar da na yanke na ficewa daga jam’iyyar, tun daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.”
Gwamna Yusuf ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da goyon bayan da ta ba shi a tsawon lokacin da yake hulɗar siyasa da NNPP.
“Ina ci gaba da nuna godiya ta gaskiya ga damar da jam’iyyar, shugabanninta da mambobinta a fadin Jihar Kano suka ba ni na kasancewa cikin tafiyar siyasar jam’iyyar tun daga 2022, tare da goyon baya, fatan alheri da hadin kai da aka nuna min a lokacin da nake cikin jam’iyyar.”
Ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da shari’o’in kotu sun dade suna girgiza tsarin jam’iyyar a fadin kasa.
“A baya-bayan nan, jam’iyyar ta fuskanci kalubale masu tsanani na cikin gida sakamakon sabanin shugabanci da shari’o’i da ake ci gaba da yi, da dama daga cikinsu na gaban kotuna domin yanke hukunci.”
A cewarsa, wadannan sabani sun kara tsaga-tsagewa tare da raunana dunkulewar jam’iyyar.
“Kara nuna wariya da rashin jin dadin mambobi ya haifar da babbar rarrabuwar kai a cikin tsarin jam’iyyar, wanda ya jawo tsagewa masu zurfi da ke kara zama masu wahalar sulhu, tare da haifar da rashin tabbas a matakan jiha da kasa baki daya.”
Gwamna Yusuf ya ce ya yanke shawarar ne bayan zurfin tunani, kuma bisa la’akari da muradin jama’a kawai.
“Bayan yin nazari mai zurfi, kuma ba tare da tauye ikon jam’iyyar na magance matsalolinta na cikin gida ba, na yanke shawarar cewa ficewata ita ce mafi alheri ga al’ummar Jihar Kano.”
Ya jaddada cewa an dauki matakin cikin kyakkyawar niyya ba tare da kiyayya ko gaba ba.
“An dauki wannan shawara ne cikin kyakkyawar niyya, ba tare da wata gaba ko bacin rai ba, tare da ci gaba da jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya, hadin kai da cigaban Jihar Kano.”
Gwamnan ya fice a yau tare da ‘yan majalisar dokokin jiha 21, ‘yan Majalisar Wakilai 8, da shugabannin kananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
Sakataren jam’iyyar NNPP na mazabar Diso-Chiranchi, Hon. Kabiru Zubairu, ya karɓi wasikar ficewar, inda ya yaba wa gwamnan bisa manyan ayyukansa a fannonin ababen more rayuwa, sabunta birane, lafiya, ilimi da karfafa tattalin arziki.
“Ina goyon bayan ra’ayin Mai Girma Gwamna dangane da rikicin da ya dade yana addabar jam’iyyarmu. Duk da cewa muna iya bakin kokarinmu wajen shawo kansa, ba mu da wani zabi face mu amince da ficewar daya daga cikin gwamnonin NNPP mafi kwazo da nagarta.”
Sa hannu: Sunusi Bature Dawakin Tofa,
Darakta Janar,
Watsa Labarai da Hulda da Jama’a,
Gidan Gwamnati, Kano.
