Kwaminan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida na jahar Kano,Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya faɗi matsayinsa akan dambarwar siyasar jahar Kano, Waiya ya ce, duk inda Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya shiga yana tare da shi .
Kwamishinan ya ce bai san kowa a siyasance ba sai Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Waiya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Gwamnati da jama’a da aka gabatar a gidan Radiyon Rahma Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alkawuran da ya ɗauka sama da kaso 90 cikin 100. Kuma Gwamna Abba ba ya butulci.
Kwamishinan ya ƙara da cewa siyasa tafiya ce ta fahimta da maslahar al’umma, ba wai tsattsauran ra’ayi ba, yana mai kira ga ‘yan siyasa da magoya baya da su fifita zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar Kano.
