Kwamishinan Shari’a na jahar Kano Barrister Abdulkarim ya yi ƙarin haske akan dambarwar da aka samu jahar Kano bayan hukumar Yansanda su ka sanar da dokar nan ta hana goyon biyu akan babura masu ƙafa biyu.
Kwamishinan Shari’a ya sanar da manema labarai. A inda ya ce , ita wannan doka ta hana goyon biyu akan babura ta ta’allaka ne ga masu yin sana’ar Acaɓa kawai. Dan haka duk wanda ya san ba acaɓa ya ke yi da Babur dinsa to zai iya goyan iyalansa ko wasu mutane, amma ba da zumman sana’a irin ta acaɓa ba.
Ga yadda hirar tamu ta kasance da Kwamishinan Shari’a na jahar Kano.
Baba Comrade, E-Magazine
05/12/2025
https://www.facebook.com/share/v/1Cy7Azhjwf/

