JAWABIN ƘARSHEN SHEKARAR 2025 NA KWAMISHINAN ‘YANSANDAN JIHAR KANO, CP IBRAHIM ADAMU BAKORI, PhD, SFIPMA, MNIM, MNIPS, MASIS, KAN NASARORIN DA AKA SAMU A SHEKARAR 2025 A ƘOƘARIN YAKI DA LAIFUKA DA TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA A JIHAR KANO, WANDA AKA GABATAR A RANAR 30 GA DISAMBA, 2025, A SHELKWATAR ‘YAN SANDAN BOMPAI, KANO

Assalamu Alaikum Yan Uwa Kuma Abokan Aiki Yan Jarida;
Ina matuƙar farin cikin ganawa daku a wannan rana, a Shelkwatar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano dake Bompai, domin gabatar muku da jawabi akan yanayin tsaro a Jihar Kano, da kuma manyan nasarorin da muka samu a fannin hana aikata laifuka, da tabbatar da tsaro a shekarar 2025.
2.0 KALUBALEN DA MUKA TARAR FARKON SHEKARA: Bayan na kama aiki a ranar 17 ga Maris, 2025, a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda na 47 a Jihar Kano, na karɓi cikakken bayanai daga abokanan aiki da sauran hukumomin tsaro kan yanayin tsaron Jihar Kano. A wancan lokacin, munga akwai ƙalubalen tsaro daban-daban a ƙananan hukumomi arba’in da huɗu (44) na Jihar Kano. Daga cikinsu akwai fadace-fadacen Daba, fashi da satar wayoyin mutane, da shaye-shaye a tsakanin matasa a ƙananan hukumomi takwas (08) na Kano ta tsakiya, wato kananan hukumomin; Kano Municipal, Dala, Gwale, Fagge, Tarauni, Nassarawa, Ungoggo da Kumbotso; sai barazanar shigowar ‘yan bindiga a ƙananan hukumomi goma sha bakwai (17) na kan iyaka; da kuma rikice-rikicen manoma da makiyaya a ƙananan hukumomi goma sha tara (19) da suke tsakiya, wato wadanda ba na kan iyaka ba kuma ba na birni ba.
3.0 YANDA MUKA GUDANAR DA AIKI (ROADMAP):
Kamar yanda Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na Kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, ya bamu umarni, shawarwari yin aiki da kwarewa, mun tantance barazanar tsaron, kuma mun kawo tsare-tsare kamar haka;
i. Aiki kafada da kafada tsakanin ‘yan sanda da al’umma (Community Policing)
ii. Tattarawa da kuma amfani da bayanan sirri wajen gudanar da aikin tsaro (Intelligence-led policing)
iii. Horas da Yan Sanda akai-akai a fannoni na Gudanarwa (Administration), Ayyuka na yau da kullum (Operations), Bincike (Investigation) da kuma tattara bayanai sirri (Intelligence)
iv. Gudanar da aiki tare da sauran hukumomin tsaro, musamman sintirin haɗin gwiwa a kan iyakokin Jihar Kano
v. Kaddamarwa da faɗaɗa Sashen Yaki da Laifukan Yanar Gido (Cybercrime Unit)
vi. Wayar da kan jama’a ta rediyo, talabijin da kafafen yaɗa labarai domin ƙarfafa alaka da ‘yan sanda ta hanyar bayar da sahihin bayanai
vii. Kaddamar da “Operation Kukan Kura” domin magance Fadan Daba da kwacen wayoyin mutane.
4.0 MANYAN NASARORI A TAKAITCE:
Daga 1 ga Janairu, 2025 zuwa 30 ga Disamba, 2025, an kama mutane dubu uku da tamanin da ɗaya (3,081) da ake zargi da manyan laifuka a sassan ‘yan sanda wato ‘Police Station’ guda 78, Area Commands 11, da Rundunar Kai Daukin Gaggawa na musamman guda 7, bisa jagoranci na. An kuma kwato makamai, miyagun ƙwayoyi, dukiyoyin sata da sauran kayayyaki kamar haka:
4.1 Wadanda aka kama:
i. Mutane 146 da ake zargi da fashi da makami
ii. Mutane 50 da ake zargi da garkuwa da mutane
iii. Mutane 112 da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi
iv. Mutane 85 da ake zargi da satar motoci
v. Mutane 45 da ake zargi da satar keke napep wato Adaidaita Sahu.
vi. Mutane 83 da ake zargi da satar babura
vii. Mutane 154 da ake zargi da sata
viii. Mutane 56 da ake zargi da zamba, wato Yan Damfara
ix. Mutane 2,350 da ake zargi da harkar daba
4.2 Wadanda aka kubutar:
– An kubutar da mutane 14 da akai garkuwa dasu
4.3 Kayayyakin da aka kwato;
i. Bindigogin AK-47 guda 9
ii. Bindigogin hannu (English pistols) guda 13
iii. Bindigogin revolver guda 8
iv. Bindigogin pump action guda 3
v. Bindigogin gargajiya (revolver) guda 37
vi. Bindigogi ƙirar gida guda 26
vii. Alburusai masu rai guda 198
viii. Alburusai guda 28 na karamar bindiga
ix. Takubba (cutlasses) guda 298
x. Wukake guda 625
xi. Gatari guda 81
xii. Gora guda 88
xiii. Takubba guda 97
xiv. Karafunan kaifi guda 183
xv. Motoci guda 94
xvi. Keke napep wato Adaidaita Sahu guda 52
xvii. Babura guda 99
xviii. Shanu guda 15
xix. Wayoyin hannu guda 145
xx. Na’urorin POS guda 20
xxi. Katunan ATM guda 37
xxii. Katunan SIM guda 67
xxiii. Buhuna 4, fakiti 523 da sinki 1242 na tabar wiwi wato ‘Cannabis Sativa’
xxiv. Fakiti 358 da ƙwayoyi 67,200 na kwayar Diazepam
xxv. Katan 6, ƙwayoyi 74,750 na Pregabalin
xxvi. Katan 634, ƙwayoyi 60,300 na Tramadol
xxvii. Katan1,490 na Exol
xxviii. Kwalabe 384 na Codeine cough syrup
xxix. Katan754 na abin maye “Rubber Solution”
xxx. Kwalabe 2,450 na abin da ake zargin kwayoyine masu bugarwa
xxxi. Buhuna 7, kwalabe 2,450 na abin maye “Akuskura” da ake amfani da shi wajen maye
5.0 SHIRIN MU NA GABA:
Wadannan matakai da aka dauka, sun haifar da gagarumin nasarori, kuma ba za a dakatar da su ba; a maimakon haka za a ƙara inganta su. Shekarar 2026 na da tanade tanade na tsaro masu kyau, domin zamu faɗaɗa hulɗa da jama’a wato ‘community policing’, ƙara fadada sintiri a kowane lokaci, inganta tsarin tattara bayanan sirri, ƙara yawan jami’ai da kayan aiki a kananan hukumomin da suke kan iyaka, tare da amfani da kafafen gargajiya da na zamani wajen wayar da kan jama’a.
6.0 JAWABIN GODIYA:
Ina miƙa godiya ta musamman ga Gwamnatin Jihar Kano, al’ummar jihar, sauran hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, da na al’umma, kafafen yaɗa labarai, mambobin PCRC, ƙungiyoyin fararen hula (CSOs), ƙungiyoyin sa-kai da dukkan masu ruwa da tsaki wato masu aiki tare da al’umma ‘community policing’ bisa goyon baya, ƙarfafawa, addu’o’i da haɗin kai da ake bamu.
6.1 Haka kuma, ina godiya ta musamman ga jami’an Yan Sanda na ba, waɗanda suka sadaukar da kai wajen cimma waɗannan nasarori.
7.0 A KARSHE:
Ko shakka babu, laifuka sun ragu a Jihar Kano, an samu sabon yanayi na zaman lafiya da tsaro, wanda ke da muhimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban al’umma.
7.1 A cikin Ikon Allah, Matsalar ‘yan daba da satar wayoyi ya zama tarihi sakamakon aiwatar da “Operation Kukan Kura”; rikice-rikicen manoma da makiyaya an shawo kansu ta hanyar ganawa da al’umma; haka kuma barazanar kutsen ‘yan bindiga ta kan iyakoki an fuskance ta da hadin kai da kuma muhimmanci.
7.2 A Saboda haka, muna da dalilai masu yawa na gode wa Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) bisa waɗannan nasarori.
8.0 Manyan Yan Jarida, ina godiya ƙwarai da gaske da gudun mawar da kuka bamu. Allah ya kaimu Sabuwar Shekara ta 2026 Lafiya da Alkairi.
9.0 Na gode. Allah Ya Saka Da Alkairi.
