Education

COMRADE SANI HALADU GWARZO YA KAMA AIKI A MATSAYIN DARAKTAN KULA DA MAKARANTUN SAKANDIRE A KANO

IMG 20260217 WA0039
IMG 20260217 WA0039

COMRADE SANI HALADU GWARZO YA KAMA AIKI A MATSAYIN DARAKTAN KULA DA MAKARANTUN SAKANDIRE A KANO

Daga Baba Comrade, E-Magazine

17 ga Fabrairu, 2026

A ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, Comrade Sani Haladu Gwarzo ya karɓi ragamar aiki a hukumance a matsayin Daraktan Kula da Makarantun Sakandire (Director Schools Service) na Kano State Senior Secondary Schools Management Board (KSSSSMB).

Sabon Daraktan ya isa ofishinsa ne tare da rakiyar shugabar ƙungiyar shugabannin makarantun sakandire ta Jihar Kano (ANCOPSS Kano State Chapter) Comrade Uwani Ahmed Balarabe, da kuma shugabannin ƙungiyar malamai ta Nigeria Union of Teachers (NUT) reshen Jihar Kano.

Shugabar ANCOPSS, Comrade Uwani Ahmed Balarabe, ta jagoranci tawagar kai sabon Daraktan gaban Sakataren Zartarwa na KSSSSMB, Honourable Rabi’u Saleh Gwarzo. A jawabinta, Balarabe ta bayyana Comrade Sani Haladu Gwarzo a matsayin malami nagari, jajirtacce kuma amintacce, wanda ya taso tun daga matakin ƙasa (grassroots), tare da nuna cewa ANCOPSS ta yi matuƙar farin ciki da zaɓensa zuwa wannan muhimmin matsayi.

Ta ƙara da cewa dukkanin Principals na Jihar Kano na tare da sabon Daraktan, kuma za su ba shi cikakken goyon baya wajen tafiyar da aikinsa. Haka kuma ta mika godiya ta musamman ga Sakataren KSSSSMB bisa irin haɗin kai da kulawar da yake bai wa harkokin ilimi a jihar. Ta kuma ce dukkanin Principals yayansa ne .

A nasa jawabin, Sakataren KSSSSMB, Honourable Rabi’u Saleh Gwarzo, ya bayyana cewa nadin Comrade Sani Haladu Gwarzo zaɓin Allah ne, ba na mutum ba. Ya kuma ce sabon Daraktan mutum ne mai amana, wanda zai karɓi ragamar aiki daga tsohon Darakta Malam Abbas me’amana, wanda ya kammala aikinsa lafiya.

Sakataren ya jaddada cewa sabon Daraktan ya san da cewa wannan office da zai shiga akwai manyan ƙalubale a cikinsa, ganin cewa akwai sama da makarantu 900 a ƙarƙashin kulawar ofishin tare da malamai sama da 20,000. Ya bukace shi da ya yi aiki tare da sauran Daraktoci na hukumar, da ma tsofaffin shugabanni, domin ci gaba da inganta harkar ilimi a jihar.

Tsohon Daraktan Kula da Makarantu, Alhaji Abbas, a nasa jawabin, ya bayyana Comrade Sani Haladu Gwarzo a matsayin mutum mai kishi da amana, yana mai tunatar da cewa shi ne Principal mafi bajinta a Jihar Kano a shekarar 2024 bisa wani tantancewa da aka gudanar. Ya ƙara da cewa sabon Daraktan na daga cikin manyan Principals da ake girmamawa a Najeriya, tare da nuna cikakken tabbaci cewa zai iya ɗaukar nauyin wannan matsayi.

A martaninsa, sabon Daraktan, Comrade Sani Haladu Gwarzo, ya mika godiya ga gwamnati, hukumar KSSSSMB, da dukkan ƙungiyoyin malamai bisa amincewa da aka yi masa. Ya bayyana cewa ƙofarsa a buɗe take ga shawarwari masu ma’ana, tare da roƙon tsohon Darakta Malam Abbas da ya ci gaba da ba shi shawarwari duk da ritayarsa.

Ya kuma nemi haɗin kan dukkan Daraktoci da malamai, yana mai cewa duk inda aka ga kuskure a kira shi a faɗa masa domin gyara, domin cimma nasarar da ake buri a harkar ilimi ta Jihar Kano.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *