ƘARANCIN MASU KAƊA ƘURI’A YA BAYYANA A ZAƁEN CIKE GURBI NA KANO MUNICIPAL DA UNGOGO
Daga Baba Comrade, E-Magazine
21 ga Fabrairu, 2026
An gudanar da zaɓen cike gurbi a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu, 2026, a ƙananan hukumomin Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano.

Zagaye da bibiyar yadda zaɓen ke gudana ya nuna cewa an fuskanci ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a yawancin rumfunan zaɓe da aka ziyarta a ƙaramar hukumar Kano Municipal. Daga cikin mazaɓun da aka kai ziyara akwai Dan’agundi, Kwalli, Gidan Makama, Shahurci, Zage da Chedi, inda aka lura da rashin fitowar jama’a yadda ake tsammani.
Haka zalika, a ƙaramar hukumar Ungogo ma an samu irin wannan yanayi a wasu mazaɓu. A mazaɓar Tudun Fulani, rahotanni sun nuna cewa masu kaɗa ƙuri’a sun yi ƙasa. Sai dai a mazaɓar Rijiyar Zaki, an samu ɗan ƙarin fitowar masu zaɓe idan aka kwatanta da sauran wuraren da aka ziyarta.
Rahotannin sun nuna cewa duk da cikar shirye-shiryen gudanar da zaɓen a wuraren da aka duba, fitowar masu zaɓe bai kai yadda ake fata ba a yawancin rumfunan zaɓe.
Ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su yi nazari kan dalilan da suka haddasa ƙarancin fitowar jama’a domin ƙarfafa guiwar al’umma a zaɓuɓɓukan da za su biyo baya.
Wani daga cikin masu zaɓen kuma Agent ya bayyana mana cewa, ” dalilin da ya sa mutane basu futo ba, shi ne jam’iyyun siyasa ba su nemi hadinkan wakilan jam’iyyun ba , wanda hakan ne ya sa jama’a ba su samu labarin wannan zaben na cike gurbi ba.”
