Politics Uncategorized

Gwamna Yusuf Ya Miƙa Sunan Murtala Garo zauren Majalisar dokokin jahar Kano domin tabbatar da shi a Matsayin Mataimakin Gwamna

IMG 20260422 WA0005
IMG 20260422 WA0005

Gwamna Yusuf Ya Miƙa Sunan Murtala Garo zauren Majalisar dokokin jahar Kano domin tabbatar da shi a Matsayin Mataimakin Gwamna

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Alhaji Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin Mataimakin Gwamna.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu.

Naɗin ya yi daidai da Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa gyara), wanda ya bai wa gwamna ikon naɗa mataimakin gwamna idan kujerar ta zama babu mai riƙe da ita.

Kujerar ta zama babu kowa ne bayan murabus ɗin da tsohon Mataimakin Gwamna, Kwamared Abdussalam Gwarzo, ya yi da kansa a ranar 27 ga Maris, 2026.

Bayan tattaunawa mai faɗi da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya roƙi Majalisar da ta bayar da amincewar da ta dace ga naɗin Garo.

Murtala Sule Garo mai shekaru 48 ƙwararren ɗan siyasa ne kuma gogaggen mai gudanar da mulki, wanda ya shafe sama da shekaru ashirin yana aiki a mukaman zaɓe da na naɗi.

Ya taɓa zama Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyarsa a jihar, mai ba gwamna shawara na musamman, sannan kuma an zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo.

Haka kuma ya yi aiki a matsayin Shugaban ALGON a Kano, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, da kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Naɗin nasa na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci da kuma tabbatar da ingantaccen isar da ayyuka ga al’ummar Jihar Kano.

Sa hannu:

Mustapha Muhammad

Babban Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna

Gwamnatin Jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *