Education

AN KAMMALA BAWA SABBIN MALAMAN MAKARANTA NA ƘANANAN HUKUMOMIN GWALE DA KUMBOTSO DA MADOBI HORO NA WUNI BIYU AKAN SANIN MAKAMAR AIKIN KOYARWA WANDA HUKUMAR ILIMIN BAIƊAYA TARE DA HADIN GUIWA DA KUNGIYAR NUT DA PLANE SUKA SHIRYA

IMG 20260106 124915 181
IMG 20260106 124915 181

AN KAMMALA BAWA SABBIN MALAMAN MAKARANTA NA ƘANANAN  HUKUMOMIN GWALE DA KUMBOTSO DA MADOBI HORO NA WUNI BIYU AKAN SANIN MAKAMAR AIKIN KOYARWA, WANDA HUKUMAR ILIMIN BAIƊAYA TARE DA HADIN GUIWA DA NUT DA PLANE SUKA SHIRYA .

aiposter 2026 01 05 092429

A ranar Talata 6/1/2026 a ke cikin rana ta biyu da ake bawa sabbin malaman makaranta 4315 horo na musamman akan dabarun koyarwa da hukumar ilimin baiɗaya ta ɗauka .

IMG 20260106 124954 002

aiposter 2026 01 06 072539

A rahotannin da muka ɗauko , mun tattauna da shugaban ilimin baiɗaya na jahar Kano Alhaji Yusuf Kabir a inda mu ka zaga da shi a ita wannan santar horon da aka samar a makarantar Dukawuya Girls Science Project dake karamar hukumar Gwale.

IMG 20260106 124553 236

aiposter 2026 01 06 072723

Ga irin abun da shugaban ya ke cewa:

Shugaban ilimin baiɗaya Alhaji Yusuf Kabir ya ce yana jan kunne ga malaman da su yi aiki da abun da aka koya musu . Kuma su yi ƙoƙari su riƙe aikinsu tsakani da Allah.

IMG 20260106 124022 717

aiposter 2026 01 06 073229

Ya ce , duk wadanda su ke yin aiki fiye da daya su tabbatar suna sauke aikin da aka dauke na koyarwa fiye da sauran aikin da suke yi ko da kuwa kasuwanci ne. Domin shi ba zai hana su yin wata sana’ar ba . Saboda halin da ake ciki na matsin rayuwa . Amma a sani duk abun da za a samu matukar ba a sauke hakkin koyarwa ba , to wannan kuɗin iska ce , dan ba za su yi albarka ba. Dan haka dole ne a bi dokokin Gwamnati na kundin tsarin aiki. Domin ku kayan gwamnati ne.

IMG 20260106 124632 051

aiposter 2026 01 06 073447

Kabir ya ƙara da cewa, dole a taimaki yara kuma kar a dinga dukansu da tsoratar da su . Domin duk malamin da ya ke tsoratar da yara ya zama tamkar terrorist kuma ya nuna shi ba kwararren malami ne ba. Dan haka ku ja yaranku dalibai a jikinku, ku nuna musu yadda za su koyi abun da ake koya musu tare da basu shawara da jansu a jika.

IMG 20260106 130636 731

Shugaban ya kuma sanar da malaman cewa, mutanan da su ka nemi wannan aikin sun kai kimanin 16,000 amma iya ku 4315 ne kacal aka iya dauka. Dan haka ku gode wa Allah da ya baku sa’ar samun nasara. Kuma yanzu duk wanda za a dauka aiki sai an yi masa jarabawa da Na’ura mekwakwalwa(CBT) kafin a ɗauke shi aiki bayan ya ci jarrabawar. Dan yanzu zamani ya canza komai ya koma amfani da na’ura mekwakwalwa.

Sannan kuma ya ce duk wanda bashi da Education ba za mu bashi confirmation letter ba, dan haka duk wanda bashi da Education to ya je ya karo karatu akan shedar koyarwa.

Kabir ya kammala jawabinsa da cewa, hukuma ba za ta yadda ake zama a staff room ana ta hira a maimakon shiga aji.

Kabir ya ce shi fa sana’ar koyarwa ya sani kuma ita ya iya tun daga shekarar 1979 a lokacin da ya samu shaidar koyarwa ta NCE. Kuma ya ce babu abun da be samu ba a harkar koyarwa.

Shugaban na hukumar ilimin baiɗaya ya zagaya dukkanin ajujuwan da ake gabatar da wannan bitar ɗaya bayan ɗaya tare da yi wa malaman tambayoyi irin na assessment akan abubuwan da aka koya musu na dabarun koyarwa da sanin makamar aiki bisa rakiyar Sakatarorin ilmi na karamar hukumar Gwale da Kumbotso da Madobi.

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar Sakatarorin ilmi na 44LGEA na jahar Kano Comrade Muntari Inuwa ya yi nasa bayanin a inda ya ke cewa, muna yi wa Allah godiya da ya bamu jajirtaccen gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda ya fidda ilimi kunya. Domin tun farkon zuwansa ya fara ɗaukan malaman makaranta sama da 5000 wanda a yanzu kuma ya sake ɗaukan sabbin malamai 4315 waɗanda su ake ba wa bita ta musamman a daidai wannan lokaci. Dan haka Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi abun a yaba kwarai.

aiposter 2026 01 07 080646

Baba Comrade, E-Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *