News

Muna bukatar Adalci akan Kisan Gillar da aka yi wa Malamar Addini, lallai a Binciki DPO – iyali

1782074628587
1782074628587

Muna bukatar Adalci akan Kisan Gillar da aka yi wa Malamar Addini, lallai a Binciki DPO

An shiga jimami da ɓacin rai bayan rasuwar Malama Ummulkhairi, wadda ta ke malamar makarantar Islamiyya kuma uwargida, wadda aka kashe ta cikin mummunan hali a wani lamari mai tayar da hankali bayan an zarge ta da satar yara ba tare da wata hujja ba.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar ta fita daga gidanta ne domin halartar wani darasin addini, amma ta kasa gane hanyar zuwa wajan wa’azin, a inda ta nemi a nuna mata hanya. A wannan lokaci ne wasu mutane suka zarge ta da satar yara, lamarin da ya haddasa tarzomar jama’a.

Ko da yake an ce an kai ta ofishin ‘yan sanda, kuma wasu sun bayar da shaida cewa fitacciyar malama ce, hakan bai hana wasu fusatattun matasa kai mata hari ba. An ce lamarin ya faru ne a bainar jama’a, kusa da ofishin ‘yan sanda, inda aka kashe ta sannan aka kona gawarta nan take. Masu lura da al’amura sun yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da yin tambayar yadda irin wannan tashin hankali zai faru kusa da ofishin ‘yan sanda.

Iyalan marigayiyar sun bukaci hukumomin ‘yan sanda da su kaddamar da cikakken bincike tare da daukar mataki kan DPO mai kula da yankin Marabar Jos a Jihar Kaduna. Haka kuma sun nemi a kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki a kuma gurfanar da su gaban kuliya, tare da biyan diyya.

Malama Ummulkhairi ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya da dama. Rasuwarta ta jefa iyalanta, dalibanta da al’umma baki daya cikin matsanancin jimami.

Allah Ya jikanta da rahama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *