NUT Kano na yi wa Malamai Fatan Alkhairi, Allah Ya Karɓi Ibadun watan Ramadan
Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Kano na taya ɗaukacin malaman makaranta murnar fara azumin watan Ramadan tare da yi musu fatan alkhairi, inda ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya karɓi ibadunsu baki ɗaya.
Shugaban ƙungiyar na Jihar Kano, Comrade Baffa Ibrahim Garko, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, 19 ga Fabrairu, 2026. Ya ce a madadin shugabannin ƙungiyar na ƙasa da na jiha, da kuma dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, suna miƙa saƙon fatan alkhairi ga malaman makaranta, gwamnatin Jihar Kano, da dukkan shugabannin hukumomin ilimi na jihar.
Ya roƙi Allah da Ya sa an fara azumin watan Ramadan cikin sa’a, tare da fatan ya karɓi ibadu da addu’o’in al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Godiya ga Gwamnati da Hukumomin Ilimi
Comrade Garko ya yi godiya ta musamman ga dukkan malaman makaranta bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa ƙungiyar, yana mai cewa addu’a ce ginshiƙin nasarorin da ake samu.
Haka kuma, ya miƙa saƙon godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ‘yan majalisarsa, tare da Kwamishinan Ilimi, Ali Haruna Makoda, bisa amincewa da shigar da kuɗaɗen karin girma (promotion) na malaman makaranta daga shekarar 2024 zuwa 2025.
Ya kuma gode wa Shugaban Hukumar Ilimin Baiɗaya, Yusuf Kabir, Shugaban Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandire, Rabiu Saleh Gwarzo, da Shugaban Hukumar Kimiyya da Fasaha, Farfesa Dahiru Saleh Muhammad, bisa goyon baya da amincewar da suka bayar wajen tabbatar da haƙƙin malaman makaranta.
Kira Ga Malamai
Shugaban ƙungiyar ya buƙaci malaman makaranta da su ci gaba da yi wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’a, domin Allah Ya ba ta ikon sauke dukkan haƙƙoƙin malaman makaranta cikin nasara, musamman a ɓangaren daidaita albashi da walwala.
A ƙarshe, Comrade Garko ya sake jaddada fatan alkhairi ga daukacin malamai tare da addu’ar Allah Ya karɓi ibadu.
Ameen.
Sa hannu:
Comrade Baffa Ibrahim Garko
State chairman
