News

ƘUNGIYAR NUT SHIYYAR RANO TA GUDANAR DA TARONTA A KARAMAR HUKUMAR KURA

images (18)
images (18)

ƘUNGIYAR NUT SHIYYAR RANO TA GUDANAR DA TARONTA A KARAMAR HUKUMAR KURA

Haɗakar Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) shiyyar Rano, wadda ta ƙunshi ƙananan hukumomi tara (9) a Jahar Kano, ta gudanar da taron shiyyarta a ranar Lahadi, 11 ga Janairu, 2026 a karamar hukumar Kura. Taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙungiyar da kuma dabarun inganta walwala da ayyukan malamai.

IMG 20260111 WA0050
Comrade Muhammad Hambali Abubakar, NUT National Vice President

Yayin taron, Mataimakin Shugaban ƙungiyar NUT na ƙasa, Comrade Muhammad Abubakar Hambali, ya jaddada muhimmancin shirya tarurruka na musamman ga Shugabannin Makarantu (Head Teachers da Principals). Hambali ya bayyana cewa irin waɗannan taruka za su taimaka wajen tsara manufofi da tsare-tsare da za su ƙarfafa ayyukan ƙungiyar da haɓaka fahimtar malamai game da aikinta.

IMG 20260111 WA0051

IMG 20260111 WA0045

Haka zalika, Sakataren walwala na ƙungiyar NUT na Jihar Kano, Comrade Bala Ali, ya bukaci ƙungiyar da ta fi mayar da hankali wajen amfani da kafafen yaɗa labarai  zamani domin yaɗa abubuwan da take yi. Ya ce hakan zai taimaka wajen warware ƙaryar da ake yaɗawa kan ƙungiyar, da kuma bayani kai tsaye ga malamai kan irin kokarin da ake yi.

IMG 20260111 WA0048

Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga dukkan ƙananan hukumomi tara (9) da ke ƙarƙashin shiyyar ta Rano da kuma wakilai na shugabancin ƙungiyar ta jahar Kano.

Comrade Iliyasu Dauda

NUT Press, Kura Branch

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *