ƘUNGIYAR NUT SHIYYAR RANO TA GUDANAR DA TARONTA A KARAMAR HUKUMAR KURA
Haɗakar Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) shiyyar Rano, wadda ta ƙunshi ƙananan hukumomi tara (9) a Jahar Kano, ta gudanar da taron shiyyarta a ranar Lahadi, 11 ga Janairu, 2026 a karamar hukumar Kura. Taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙungiyar da kuma dabarun inganta walwala da ayyukan malamai.

Yayin taron, Mataimakin Shugaban ƙungiyar NUT na ƙasa, Comrade Muhammad Abubakar Hambali, ya jaddada muhimmancin shirya tarurruka na musamman ga Shugabannin Makarantu (Head Teachers da Principals). Hambali ya bayyana cewa irin waɗannan taruka za su taimaka wajen tsara manufofi da tsare-tsare da za su ƙarfafa ayyukan ƙungiyar da haɓaka fahimtar malamai game da aikinta.
Haka zalika, Sakataren walwala na ƙungiyar NUT na Jihar Kano, Comrade Bala Ali, ya bukaci ƙungiyar da ta fi mayar da hankali wajen amfani da kafafen yaɗa labarai zamani domin yaɗa abubuwan da take yi. Ya ce hakan zai taimaka wajen warware ƙaryar da ake yaɗawa kan ƙungiyar, da kuma bayani kai tsaye ga malamai kan irin kokarin da ake yi.
Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga dukkan ƙananan hukumomi tara (9) da ke ƙarƙashin shiyyar ta Rano da kuma wakilai na shugabancin ƙungiyar ta jahar Kano.
Comrade Iliyasu Dauda
NUT Press, Kura Branch