MAKON YANJARIDA 2025
Ƙungiyar yanjaridu ta jahar Kano ta bude taronta na makon yanjarida na shekarar 2025 da addu’ar neman zaman lafiya.
Kungiyar ta gabatar da taron addu’ar ne a ranar 5/12/2025 a harabar ƙungiyar yanjaridu(NUJ) ta jahar Kano da ke Farm Center da misalin ƙarfe 9:00 na safe. A inda manyan malamai da yanjaridu na bangare da dama su ka samu damar halarta bisa jagorancin shugaban Uwar kungiyar ta jahar Kano Comrade Sulaiman Dederi da mataimakansa. Malaman da su ka jagoranci zaman addu’ar sun haɗa da Malam Gwani Nasir.
Comrade Dederi ya ce Wannan taro na makon yanjarida shi ne na farko a tarihin jahar Kano, wanda hakan ne ya sa aka fara buɗe taron da taron addu’a ta musamman akan hadinkan yanjarida da nema wa jahar Kano zaman lafiya da ma ƙasa baki daya. Comrade Dederi ya ƙara da ce wa, “wannan


shagulgula na makon yanjarida za a gabatar da abubuwa kamar haka:
1- Taron addu’a
2- Wasan ƙwallon ƙafa
3- Ziyarar marasa lafiya da kuma
4- Buɗe ofishin yanjarida na ɓangaren yanar Gizo-gizo.
Comrade Dederi ya kammala jawabinsa da ce wa, za a ci gaba da yin wadannan taruka na Makon yanjarida a duk shekara.
Baba Comrade, E-Magazine
05/12/2025
