Education

ES FORUM ta Yaba wa Gwamna Abba Kan Amincewa da biyan Haƙƙoƙin Ƙarin Girma ga Ma’aikatan LGEA a Kano

IMG 20260212 WA0014
IMG 20260212 WA0014

ES FORUM ta Yaba wa Gwamna Abba Kan Amincewa da biyan Haƙƙoƙin Ƙarin Girma ga Ma’aikatan LGEA a Kano

Ƙungiyar Sakatarorin Ilimi (ES) mai wakiltar Hukumomin Ilimi na Ƙananan Hukumomi 44 (LGEAs) na Jihar Kano ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawarinsa na amincewa da fitar da kuɗaɗen haƙƙoƙin ƙarin girma ga malaman makarantun firamare da sauran ma’aikatan LGEA a faɗin jihar.

Yabon ya fito ne ta bakin Shugaban kungiyar na rikon ƙwarya, Kwamared Nura Sulaiman, wanda ya jinjina wa Gwamnan bisa cika alkawarinsa ga dubban ma’aikatan ilimi. Ya bayyana matakin a matsayin wata shaida karara ta jajircewar Gwamna Abba wajen kula da jin daɗin ma’aikata da kuma ƙudurin sa na ƙarfafa ɓangaren ilimi a Jihar Kano.

Kwamared Sulaiman ya ƙara da cewa amincewa da biyan haƙƙoƙin ƙarin girman ya sake tabbatar da martabar Gwamnan a matsayin shugaba mai cika alƙawari kuma mai kishin ci gaban ilimi. A cewarsa, wannan mataki ya ƙara ɗaga ƙwarin guiwa da kuzari a tsakanin malamai da sauran ma’aikatan ilimi a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Ƙungiyar ta kuma miƙa godiya ta musamman ga Shugaban Hukumar Ilimi na Bai-ɗaya na Jihar Kano (SUBEB), Alhaji Yusuf Kabir, bisa ƙoƙarinsa na ganin an haɗa kuɗaɗen haƙƙoƙin ƙarin girman malamai cikin albashin watan Fabrairu na shekarar 2026. Sakatarorin sun bayyana gamsuwarsu da salon jagorancinsa da kuma jajircewarsa wajen bunƙasa ilimin bai-ɗaya a jihar.

A ƙarshe, kungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga duk wasu tsare-tsare da manufofi da ke nufin inganta jin daɗin malamai tare da ɗaga darajar ilimi a Jihar Kano.

Sa hannu:

Kwamared Nura Sulaiman

Shugaban Dandalin ES na rikon ƙwarya

Jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *