Interview

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Online Kano Ta Jaddada ƙudurinta na  bin Ka’idojin Aikin Jarida tare da yin Allah wadai ga mutanen da ke Aikin jarida domin  Batanci ga wani ko hukuma– Dangambo

kanoonlinemediachapel20251205 2124383494403415546403549 (1)
kanoonlinemediachapel20251205 2124383494403415546403549 (1)

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Online Kano Ta Jaddada ƙudurinta na  bin Ka’idojin Aikin Jarida tare da yin Allah wadai ga mutanen da ke Aikin jarida domin  Batanci ga wani ko hukuma– Dangambo

Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida na Sashen Online da ke ƙarƙashin Ƙungiyar ta Ƙasa  ‘(NUJ) reshen Kano, Abubakar Abdulqadir Dangambo, ya bukaci mambobinsa da su ci gaba da bin ƙa’idoji da ka’idojin aikin jarida na gaskiya da rikon amana.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Kano, ranar Juma’a.

Dangambo ya bayyana yadda wasu Editocin kafafen labarai na Online ke amfani da sunayen ƙarya (pseudonyms) wajen yi wa mutane da hukumomi batanci  wanda hakan  ya sabawa ka’idojin aikin jarida.

“Aikin jarida yana buƙatar daidaito (balancing), ba za ka iya bayar da labarin gefe guda kawai a cikin rikici ba, saboda hakan yana iya sa a zarge ka da nuna bangaranci. Abin takaici, wasu suna ɓoye sunansu a ƙarƙashin Kano suna yada labaran karya da suka sabawa ƙa’ida da ɗabi’ar aikin jarida.”

“Aikin jarida alama ce ta cigaba, idan ‘yan jarida suka kasance masu gaskiya da bin ƙa’ida wajen gudanar da aikinsu, to wannan shi ne tubalin cigaba.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan jarida na Online waɗanda har yanzu ba su yi rijista da kungiyar ba , da su gaggauta yin rejista. Dan ba za a zauna ana kallo ba yayin da wasu ke bata sunan aikin jarida ta hanyar aikata rashin da’a.

“Wadannan kafafen labarai na Online sun san kansu, ya kamata su garzayo su yi rijista da mu nan da nan, domin yanzu haka muna kan aiki na wallafa sunayen mambobinmu.”

Dangambo .

05/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *