Featured

Wani Mazaunin Dorayi Ya Roki Gwamna Abba Yusuf da ya Duba Batun Gidansa Da Ake Cewa Ginin Ofishin ’Yan Sanda yai iyaka da shi

17880290870813120765133671564835
17880290870813120765133671564835

Wani Mazaunin Dorayi Ya Roki Gwamna Abba Yusuf da ya Duba Batun Gidansa Da Ake Cewa Ginin Ofishin ’Yan Sanda yai iyaka da shi

KANO — Wani mazaunin Unguwar Dorayi a Jihar Kano, Usman Alhaji Ya’u Dorayi, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya sa baki tare da duba halin da yake ciki sakamakon gina sabon ofishin ’yan sanda a yankin da aka yi na VCRU.

Usman Alhaji Ya’u, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin mazauna yankin da aka gina ofishin ’yan sandan, ya ce gidansa da na wani makwabcinsa cewa, suna fuskanci matsala sakamakon wannan Police station.

A cewarsa, an yi masa bayani cewa za a sayi gidansa dan a yi amfani da wurin wajen gina ofishin ’yan sanda, amma ya ce yadda aikin ya gudana ya haifar da barazana ga gidansa, kuma har yanzu ba a sai gidan nasa ba.

Ya ce: “Ina kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano da ya taimaka mana, ya zo ya duba ya gani da idonsa halin da muke ciki.”

Usman ya kuma bayyana cewa an taba tattaunawa da su kan aikin, amma a cewarsa, abubuwan da suka biyo baya ba su kasance kamar yadda aka fahimta a farkon tattaunawar ba.

Ya roƙi Gwamna Abba Yusuf da ya tura jami’ai ko wakilansa domin su je wurin su ga halin da gidajen suke ciki tare da nemo hanyar da za a warware matsalar cikin adalci.

“Don Allah, don Annabi, ina roƙon Mai Girma Gwamna ya taimaka mana. Ko wane jami’i nasa ya zo ya gani da kansa halin da muke ciki,” in ji shi.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ake amfani da wurin,.

Usman ya jaddada cewa ba ya adawa da samar da ofishin ’yan sanda. Sai dai yana son gwamnati ta duba tasirin aikin ga gidajensu tare da tabbatar da cewa an yi abin da ya dace.

Ya ƙara da cewa samar da tsaro abu ne mai muhimmanci ga al’umma, amma ya kamata a gudanar da irin waɗannan ayyuka ta yadda ba za su jefa wasu mazauna cikin matsala ba. Ya kuma ce ruwan da ya ke sauka a offishin yansandan yana sa gidansa cikin danshi da fargaba. Wanda hakan ne ya sa iyalansa su ke kwana a maƙota.

Allah ya tai maki Gwamnan jahar Kano da dukkanin abokanan aikinsa masu amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *