SHUGABANNIN DALIBAI NA JAM’IYYAR APC KANO SUN BAYYANA GOYON BAYANSU GA GWAMNA ABBA, ZA SU AIKI DA KAFAFAN YAƊA LABARAI DOMIN BAYYANA AYYUKAN GWAMNA
Masu Ruwa da Tsaki na Daliban APC na Jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

An bayyana wannan matsaya ne a ranar Juma’a, lokacin da wasu daga cikin shugabannin suka kai ziyarar ban-girma ga Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, a ofishinsa.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban ƙungiyar, Comrade Abdulrahman Bala, ya ce matsayar goyon bayan Gwamnan ta kasance baki ɗaya, kuma an ɗauki wannan mataki ne bisa la’akari da dimbin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin ke aiwatarwa.
Comrade Bala ya bayyana cewa ɓangaren ilimi a Kano ya samu kulawa da ba a taɓa ganin irinta ba a ƙarƙashin Gwamna Abba, tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantun gaba da sakandare.
Ya ƙara da cewa, ɗaliban Kano ba su da wani zaɓi face su haɗa kai wajen mara wa Gwamnan baya, domin ba shi damar ci gaba da kyawawan ayyukan da ya fara.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba ƙungiyar za ta fara gudanar da rangadin kafafen yaɗa labarai a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, domin tattara da kuma rubuta ayyukan da gwamnatin ta aiwatar, tare da wayar da kan jama’a game da nasarorin da aka samu zuwa yanzu.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaddamar da shirye-shiryen tallafa wa matasa, domin ba su damar zama masu amfani ga kansu da al’umma, tare da dogaro da kansu.
A nasa jawabin, Kwamishinan, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yaba wa ɗaliban bisa wannan shawara da ya bayyana a matsayin mai kyau, ta hanyar goyon bayan ƙoƙarin Gwamna na neman wa’adi na biyu, yana mai cewa hakan alama ce ta ƙaunar da suke yi wa ci gaban Jihar Kano.
Ya yi alƙawarin cewa Ma’aikatar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da ƙungiyar , musamman kan batutuwan da suka shafi ilimin ɗalibai, wanda ya ce yana daga cikin muhimman manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Comrade Waiya ya yi watsi da zarge-zargen da masu sukar gwamnati ke yi cewa gwamnatin ba ta damu da jin daɗin ɗaliban da ke karatu a manyan makarantun jihar ba, yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe.
Ya bayyana cewa ƙudurin gwamnatin na inganta ilimi ya bayyana ne ta hanyar ware kaso 29.4 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar ga ɓangaren ilimi, da kuma ayyana Dokar Taɓarɓarewar Ilimi (State of Emergency), baya ga wasu dimbin tsare-tsare da tallafin musamman da aka bai wa ɓangaren ilimi a jihar.
A cewar sa, sauran matakan da gwamnatin ta ɗauka sun haɗa da:
Rage kuɗin makaranta ga ɗalibai a jihar;
Biyan miliyoyin Naira na kuɗaɗen jarabawar NECO, WAEC da NBAIS ga ɗalibai;
Taimaka wa ɗaliban Kano wajen zuwa karatu a ƙasashen waje, shirin da har yanzu yake ci gaba;
Gina sabbin makarantu da gyaran tsofaffin makarantu a faɗin jihar, domin samar da ingantaccen yanayin karatu ga ɗalibai da kuma malamai.
“Wannan gwamnati ta ƙaddamar da manufofi da dama a fannin ilimi domin rage wa ɗalibai da iyaye nauyi. Har yanzu ana tura ɗaliban Kano zuwa ƙasashen waje domin karatu, kuma suna amfana da wannan shiri. Babu wani sauyi da aka yi wajen dakatar da shirin,” in ji Kwamishinan.
Ya ƙara kira ga ɗaliban da su kasance masu gaskiya, kishin ƙasa, tare da zama jakadu nagari na Jihar Kano a duk inda suka samu kansu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba su goyon baya.
Sa hannu:
BALARABE ABDULLAHI KIRU
Darakta, Wayar da Kan Jama’a
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida
Jihar Kano
21 ga Agusta, 2026
