Education

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR D/KUDU YA KAMMALA GYARAN HUKUMAR ILIMI TA ƘARAMAR HUKUMAR D/KUDU

images (33)
images (33)

Ilimi gatan al’umma, a ranar Talata 30/12/2025 shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Hon. Sani Ahmed Mairago yai bikin buɗe hukumar ilimin baiɗaya daya gyara cikin ƙankanin lokaci .

IMG 20251230 WA0031

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce Wannan aiki ba shi ne na farko ba. Domin an gyara makarantu da dama da kuma sama musu kayayyakin koyo da koyarwa. Mairago ya ƙara da cewa, Gwamnatin Alh Abba Kabir Yusuf gwamnati ce me son hidimta wa ilimi tun daga tushe.

IMG 20251230 WA0042
Comrade Baffa Ibrahim Garko, NUT Chairman 

Merago, ya sake nanata cewa, bashi da wani burin da ya wuce ya ga ya taimaka wa malaman makaranta da kuma gyara duk wata makaranta da ta ke neman ɗauki da kuma gina sabbin ajujuwan karatu .

Shugaban ƙungiyar malaman makaranta na jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko ya yi godiya tare da nuna farin cikinsu wajan ganin yadda shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Alh. Sani Ahmed Mairago ya sabunta hukumar ilimin ta Dawakin Kudu.

images (31)
Hon Lamido Sunusi, Warawa LGA chairman 

Garko ya ce, dole ne a yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Hon Sani Ahmed Mairago. Garko ya tabbatar wa da manema labarai cewa, kungiyar NUT ta jahar Kano za ta karrama shugaban ƙaramar hukumar a ranar bikin ranar malamai ta Duniya da za a gabatar a shekara me zuwa (2026) duba da irin namijin kokari da shugaban ke yi na ciyar da ilimi gaba da kuma wannan katafaran gyaran LGEA da ya yi , wanda babu wata karamar hukuma da tai irinsa.

Haka zalika shugaban ƙaramar hukumar Warawa Hon Lamido Sunusi Ahmed wanda shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a wannan taro, a inda ya ce, ” ina kira ga malaman makaranta da ku rike aikinku da gaskiya tare da taimakawa ɗalibai.

Shugaban ƙungiyar NUT reshen karamar hukumar Dawakin Kudu ya yi jawabin godiya ga shugaban ƙaramar hukumar na Dawakin Kudu.

Baba Comrade, E-Magazine

30/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *