EID MESSAGE

Saƙon Sallah: Shugaban NUT Kano Ya Taya Gwamna, Malamai Murna, Ya Jinjinawa Shugabannin Ƙungiya a Ƙananan Hukumomi 44

1774006926306
1774006926306

Saƙon Sallah: Shugaban NUT Kano Ya Taya Gwamna, Malamai Murna, Ya Jinjinawa Shugabannin Ƙungiya a Ƙananan Hukumomi 44

Shugaban Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT), reshen Jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, ya miƙa saƙon taya murnar Sallah ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano, da Sarkin Kano, Alhaji Sunusi Lamido Sunusi, tare da shugabanni na dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

A cikin saƙonsa, Kwamared Garko ya kuma taya muhimman masu ruwa da tsaki a fannin ilimi murna, musamman Kwamishinan Ilimi, Dakta Ali Haruna Makoda, da dukkan malamai a faɗin Jihar Kano, shugabannin NUT na Branches, da al’ummar Musulmi a duniya baki ɗaya, a wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

Ya bayyana matuƙar godiya ga shugabannin NUT na dukkan rassan ƙananan hukumomi 44 bisa haɗin kai, jajircewa, da goyon bayan da suke bai wa malamai ba tare da gajiyawa ba. Ya kuma yaba da ƙoƙarinsu wajen bayar da tallafin azumin Ramadan da gudanar da ayyukan jin ƙai, musamman wajen tallafa wa iyalan malamai da suka rasu.

Kwamared Garko ya kammala da addu’ar Allah Ya karɓi ibadun bayinsa, Ya sanya su cikin waɗanda aka gafarta musu, kuma Ya zaɓe su cikin bayinsa na gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *