BA GASKIYA BA NE ZANCEN ZA MU DAKATAR DA AIKI DAGA DAYA GA WATAN SATUMBA, 2026 , A GUJI JITAJITA
Kamfanin Opay ya tabbatar da cewa, ba su da masaniyar wata takarda da ta ke yawo mai ɗauke da saƙon dakatar da aikin Bank na Opay daga ranar 1/8/2026. Kamfanin ya ce wannan takarda ba daga kamfanin Opay ta ke ba. Kuma Company yana nan cikin aminci. Dan haka kowanne abokin huldarsu da su kwantar da hankalinsu, kuma babu maganar umarnin kowa ya kwashe kudinsa daga ma’ajiyarsa ba.
Kamfanin ya kuma yi kira ga abokan huldarsu da su guji duk yada Wata jitajita a social media.
