ƘUNGIYAR KWANKWASIYYA-SHEKARAU TA CANZA SUNA ZUWA ABBA GIDA GIDA-SHEKARAU, TA BAYYANA CIKAKKEN GOYON BAYANTA GA GWAMNA ABBA KABIR YUSUF GABANIN ZAƁEN 2027
Ƙungiyar Dandalin Haɗin Kan Kwankwasiyya-Shekarau Unity Forum ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da sauya sunan ƙungiyar zuwa “Abba Gida-Gida – Shekarau Unity Forum” domin ci gaba da marawa Gwamnan baya gabanin Babban Zaɓen 2027.

Dandalin ya bayyana wannan matsaya ne a ranar Litinin yayin wata ziyarar goyon baya da mambobinta suka kai wa Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a ofishinsa.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban Dandalin, Alhaji Ahmed Saminu (DOC), ya bayyana cewa an kafa Dandalin ne bayan haɗewar wasu jiga-jigan jam’iyyun APC da PDP a shekarar 2023 domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.
Ya ce:
«”Ko bayan jagoranmu, Malam Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam’iyyar, mu mun ci gaba da kasancewa cikin tafiyar Kwankwasiyya. Sai dai abin takaici, ba a ba mambobinmu damar cin moriyar irin gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar wannan tafiya ba.»
«Amma yanzu, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kusantar da mu da gwamnati tare da ba mu muhimmancin da ya dace. Saboda haka muka zo yau domin bayyana cikakken goyon bayanmu ga Alhaji Abba Kabir Yusuf tare da sauya sunan Dandalinmu zuwa ‘Abba Gida-Gida – Shekarau Unity Forum.'”»
Alhaji Ahmed Saminu ya ce Dandalin na da cikakken yaƙinin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cancanci cikakken goyon baya domin ci gaba da ayyukan alheri da ya fara tun bayan hawansa mulki, waɗanda suka sanya Jihar Kano ta zama wuri mai ci gaba da kyakkyawan yanayin rayuwa.
Ya yabawa Gwamnan kan nasarorin da ya samu a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, lafiya, tsaro, ƙarfafa matasa da mata, gina hanyoyi da samar da muhimman ababen more rayuwa.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan nasarori ne suka ƙarfafa Dandalin wajen bayyana biyayyarsu ga Gwamnan ta hannun Kwamishinan, wanda ya ce ya kasance yana wayar da kan jama’a game da kyawawan manufofi da shirye-shiryen wannan gwamnati.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya gode wa mambobin Dandalin bisa kasancewarsu ‘yan siyasa masu hangen nesa da suka zaɓi abin da ya dace domin ci gaban Jihar Kano.
Ya ce matakin da suka ɗauka na mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya domin wa’adi na biyu ya nuna irin kishinsu ga ci gaban jihar.
Kwamared Waiya ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shugaba mai sanin abin da ya dace, wanda a ko da yaushe yake ƙoƙarin tabbatar da cewa al’ummar Kano suna amfana da ribar dimokuraɗiyya.
Ya ce:
«”Duk abin da maƙiyan jihar ke faɗi game da Gwamnan ba zai taɓa karkatar da shi daga ƙudurinsa na samar wa al’ummar Kano ingantaccen shugabanci ba.”»
Ya kuma tabbatar wa Dandalin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin aiki tare da su domin tabbatar da nasara a Babban Zaɓen 2027.
Kwamishinan Ya Karɓi Baƙuncin Ƙungiyar Trusted Youth Awareness for Abubakar Kabir Abubakar Bichi
A wani ci gaba mai alaƙa da hakan, Kwamishinan ya kuma karɓi baƙuncin mambobin Trusted Youth Awareness for Abubakar Kabir Abubakar Bichi, waɗanda suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.
Da yake magana a madadin tawagar, Shugaban ƙungiyar, Farouk Muhammad Dangora, ya ce sun kai ziyarar ne domin bayyana goyon bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf gabanin Babban Zaɓen 2027.
Ya yabawa Gwamnan bisa ƙoƙarin da ya yi wajen biyan haƙƙoƙin tsoffin kansiloli, waɗanda suka shafe lokaci cikin mawuyacin hali sakamakon matsin tattalin arziki.
Farouk ya kuma jinjinawa gwamnatin bisa manyan nasarorin da ta samu a fannoni daban-daban na ci gaban al’umma, waɗanda ya ce sun cancanci a ba Gwamnan wa’adi na biyu.
Haka kuma ya gode wa Kwamishinan bisa irin rawar da ya taka wajen tabbatar da biyan haƙƙoƙin tsoffin kansilolin.
Ya ce:
«”Muna roƙon Kwamishina ya zama Babban Uban Gidan (Grand Patron) ƙungiyarmu, sannan muna neman haɗin gwiwa da Ma’aikatar domin ci gaba da yaɗa kyawawan ayyukan wannan gwamnati.”»
A nasa jawabin, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana farin cikinsa da ganawa da mambobin ƙungiyar.
Ya bayyana Abubakar Kabir Abubakar Bichi a matsayin mutum abin dogaro mai kishin Kano, wanda ke aiki kafada da kafada da Mai Girma Gwamna wajen kawo ayyukan ci gaba ga jihar.
Ya ce al’ummar Kano suna alfahari da irin gudunmawar da Abba Bichi ke bayarwa a mazabarsa da ma faɗin jihar baki ɗaya, tare da tabbatar da cewa ƙofofin Ma’aikatar za su ci gaba da kasancewa a buɗe domin haɗin gwiwa wajen bunƙasa manufofi da nasarorin gwamnati.
An Sanya Hannu
Balarabe Abdullahi Kiru
Darakta, Sashen Wayar da Kan Jama’a
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano
