Security

KSSSSMB TA JA HANKALIN JAMA’A KAN DAMFARAR DA AKE YI DA SUNAN ƊAUKAN AIKI, TA TABBATAR DA KAMUN WASU MUTANE DA AKE ZARGI

1789216828408
1789216828408

KSSSSMB TA JA HANKALIN JAMA’A KAN DAMFARAR DA AKE YI DA SUNAN ƊAUKAN AIKI, TA TABBATAR DA KAMUN WASU MUTANE DA AKE ZARGI

Hukumar Kula da Makarantun Manyan Makarantun sakandare ta Jihar Kano (KSSSSMB) ta ja hankalin al’umma kan wasu mutane ko ƙungiyoyi da ke bayar da guraben aikin bogi, ko kuma suke ikirarin suna da ikon taimakawa wajen samun aiki a hukumar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a ya fitar, Babban Sakataren Hukumar, Hon. Rabi’u Sale Gwarzo, ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan, tare da dogaro da sahihan bayanai da hanyoyin daukan ma’aikata na hukuma da ake sanarwa ta hanyoyin da Hukumar da Gwamnatin Jihar Kano suka amince da su.

Babban Sakataren ya bayyana cewa daukar ma’aikata a Hukumar yana gudana ne bisa ƙa’idojin da aka amince da su da kuma bin tsarin da ya dace. Ya jaddada cewa babu wani mutum da aka ba izinin karɓar kuɗi daga jama’a ko neman kuɗi a madadin samun aiki ko kuma ba da tabbacin samun aikin yi a Hukumar.

Gwarzo ya bayyana cewa neman ko karɓar kuɗi daga mutane da sunan samar musu da aiki laifi ne da doka ta tanada hukuncinsa, tare da gargadin mutane da su guji shiga irin waɗannan ayyuka na bogi.

Ya kuma shawarci jama’a da su gaggauta kai rahoton duk wani tayin aikin bogi ko wata damfara da ta shafi daukar ma’aikata ga Hukumar ko sauran hukumomin da abin ya shafa, domin ɗaukar matakin da ya dace.

Ya bayyana cewa Hukumar ta riga ta ɗauki matakai domin dakile irin waɗannan ayyukan damfara da kuma kare jama’a daga masu yaudarar su da sunan daukar aiki.

Babban Sakataren ya yaba da ƙoƙarin hukumomin da suka dace wajen magance rahotannin damfarar da ake yi da sunan daukar ma’aikata. Ya ƙara da cewa, an kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a cikin lamarin, kuma a halin yanzu suna taimakawa wajen gudanar da bincike.

Ya tabbatar da cewa Hukumar za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga duk wani ƙoƙari na dakile damfarar daukar ma’aikata da kuma kare jama’a daga masu amfani da sunan aiki wajen yaudarar mutane.

Haka kuma, Babban Sakataren ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewarsa wajen ƙarfafa harkar ilimi, musamman ta hanyar ɗaukar ƙarin ma’aikata domin inganta koyarwa da koyo a makarantun sakandaren jihar.

Usman Datti Abdullahi

Daraktan Wayar da Kan Jama’a

KSSSSMB

11/9/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *