News

Gwamnatin jahar Kano ta Haramta samar da Kungiyar ‘Independent Hisbah Fisabilillahi’, ta kuma  ayyanata a Matsayin Ƙungiyar Da Ba Ta Da Doka . 

Gwamnatin jahar Kano ta Haramta samar da Kungiyar ‘Independent Hisbah Fisabilillahi’, ta kuma  ayyanata a Matsayin Ƙungiyar Da Ba Ta Da Doka .

1765569060570
Comrade Ibrahim Abdullahi Wariya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jahar Kano

Gwamnatin Jahar Kano ta fitar da sabon umarni da ke haramta kafawa ko gudanar da kowacce irin ƙungiya ta Hisbah da ba ta da izini, musamman wata ƙungiya da ake kiranta da suna “Independent Hisbah Fisabilillahi”.

Gwamnatin Kano

Wannan umarni da aka sanya wa suna “Kano State Government (Prohibition of the Independent Hisbah Fisabilillahi) Order 2025” Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanya wa dokar hannu, kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya sanar da manema labarai.

Kwamishina Wariya ya bayyana ce wa, umarnin ya samo asali ne daga Sashe na 5(2) na Kundin tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), wanda ya ba gwamnan jiha ikon aiwatar da doka da tabbatar da zaman lafiya da bin doka a cikin jiharsa.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta nuna matuƙar damuwa game da bayyanar wasu mutane da ƙungiyoyi da ke “daukar ma’aikata a ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna ‘Independent Hisbah Fisabilillahi’ ba tare da wani sahihin izini ba . ”

A cewarsa,kafa irin waɗannan ƙungiya tamkar ƙungiya ce da za a iya amfani da ita wajen tilastawa jama’a su bijirewa hukuma,  kuma gwamnati ta bayyana hakan a matsayin “aiki da ya sabawa doka, kuma yana iya haddasa tayar da hankali da rushe aikin hukumar Hisbah ta jihar.”

Waiya ya ƙara da cewa umarnin ya fayyace komai  karara ce wa “kafa ko gudanar da Independent Hisbah Fisabilillahi haramun ne, kuma an hana ta yin aiki ko aiwatar da kowanne irin abu a fadin jihar Kano.”

Domin ƙarfafa ikon hukuma na hukumar Hisbah ta Jihar Kano, gwamnati ta jaddada cewa “za ta ci gaba da kasancewa ita kaɗai ce hukuma ta doka da aka amince da ita a jihar” domin gudanar da ayyukan da suka shafi Hisbah.

Kwamishina Waiya ya bayyana  ce wa, wannan umarni ya ba wa dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa — ciki har da Ƴan Sanda na Najeriya, Hukumar DSS, da NSCDC — su gudanar da bincike kan wadanda suka kafa ko ke daukar nauyin ƙungiyar da aka haramta. Kuma su dakatar da duk wani aiki da ya shafi ƙungiyar, tare da ɗaukar matakan doka don hana rikici.

A cikin wani gargaɗi mai tsanani ga jama’a, Waiya ya bayyana ce wa “shiga, goyon baya ko hulɗa da ƙungiyar Independent Hisbah Fisabilillahi yana nufin karya dokar Jihar Kano.” Sannan Ya bukaci duk wanda aka ɗauka ko aka nemi ya shiga ƙungiyar da ya janye da gaggawa kuma ya kai rahoto zuwa ofishin tsaro mafi kusa, ko ofishin Hisbah, ko hukumar ƙaramar hukuma.”

Ya kuma ƙara da ce wa, duk wanda ya karya wannan umarni zai fuskanci gurfanarwa a gaban kotu bisa laifukan da suka haɗa da taro ba bisa doka ba, kwaikwayon hukuma, da kafa ƙungiyar tilasta doka ba tare da izini ba. Kalmar “Independent Hisbah Fisabilillahi” a cewar umarnin, ta shafi kowacce ƙungiya, rukunin aiki, kwamitin tilasta doka, motsi ko ƙungiya da aka tsara don yin ayyukan Hisbah ba tare da kasancewa karkashin hukumar doka ba.

“Wannan umarni na gwamnati zai fara aiki nan take, kuma za a wallafa shi a cikin gazette na Jihar Kano. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanya hannu a ranar 8 ga Disamba, 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *