Ƙungiyar NUT ta shiyyar Municipal me ɗauke da ƙananan hukumomi 7 , waɗanda su ka haɗa da KMC , Gwale , Dala Nassarawa, Kumbotso, Madobi da kuma Tarauni ta yi taronta na 9 a karamar hukumar Kumbotso.
A ranar Asabar 13/12/2025 Gamayyar kungiyar NUT tare da kungiyar AOPSHON sun tattauna akan matsalolin da malamai su ke fuskanta musamman akan yin register TIN

Shugaban shiyyar kungiyar ta Municipal Comrade Sani Kumbotso ya ce , insha Allahu za a kai waɗannan ƙorafe-ƙorafe da aka tattauna zuwa ga Uwar kungiyar ta jaha domin cimma matsaya da kuma ɗaukan matakan da su ka dace musamman ma akan registration na TIN numba da TRCN.


A wannan taro an samu halartar dukkanin jagorori na jaha da kuma trustees na dukkannin Branches.


Comrade Kabiru Garba Fagge (NUT 3rd VICE Chairman) ya yi ƙarin haske akan matsalolin da aka tattauna tare da cin alwashin ganin an taimaki malaman makaranta. Comrade Fsgge ya nemi dukkanin shugabannin NUT na kananan hukumomi da su ci gaba da ba wa sakatarorin ilimi hadin kai.

Baba Comrade, E-Magazine
13/12/2025
