eMagazine Media Channel Politics GWAMNA ABBA ZAI KOMA APC A RANAR LITININ 5/1/2026- DAILY NIG.
Politics

GWAMNA ABBA ZAI KOMA APC A RANAR LITININ 5/1/2026- DAILY NIG.

images (5)

images (5)

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zai shiga jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance a ranar Litinin, kamar yadda DAILY NIGERIAN  Ce ta ruwaito.

Gwamna Abba Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a jam’iyyar NNPP, ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen sauya shekar tasa.

Majiyoyi da ke da masaniya kan shirin sauya shekar gwamnan sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yitwalda, ne za su karɓi gwamnan a Abuja.

Rahotanni sun ce tuni dai an dawo da jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje, daga wata tafiya da yake yi a Dubai. Haka kuma an umarci shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, da ya taƙaita tafiyarsa ta Umara domin ya miƙa katin zama ɗan APC ga gwamnan a mazabarsa ta Diso, da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, a cikin makon nan.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version