eMagazine Media Channel Politics KOMISHINA WAIYA YA ZIYARCI ‘YAN KATSINA MAZAUNA KANO, YA SAKE JADDADA GOYON BAYAN GWAMNATIN GWAMNA ABBA KABIR YUSUF
Politics

KOMISHINA WAIYA YA ZIYARCI ‘YAN KATSINA MAZAUNA KANO, YA SAKE JADDADA GOYON BAYAN GWAMNATIN GWAMNA ABBA KABIR YUSUF

1767382737374197 0

1767382737374197 0

KOMISHINA WAIYA YA ZIYARCI ‘YAN KATSINA MAZAUNA KANO, YA SAKE JADDADA GOYON BAYAN GWAMNATIN GWAMNA ABBA KABIR YUSUF

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kai ziyara ta girmamawa ga ofishin ‘yan asalin Jihar Katsina mazauna Kano. A yayin ziyarar, Kwamishina Waiya ya jaddada muhimmancin ƙarfafa dangantaka tsakanin Gwamnatin Jahar Kano da al’ummar Katsina, tare da tabbatar musu cewa ƙofar gwamnatin Kano a buɗe take don sauraron koke-koke da shawarwarinsu a kowanne lokaci.

Kwamishinan ya  ƙara da cewa: “Duk lokacin da na kai wani buƙata ko ƙara wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana tabbatar da cewa an bi sahihin mataki cikin gaggawa domin warware matsalar. Wannan yana nuna irin jajircewarsa wajen kawo sauyi da inganta rayuwar al’umma. Gwamna kullum yana sauraron muradun jama’a tare da aiki ba dare ba rana don share musu hawaye.”

‘Yan Katsina mazauna Kano sun nuna jin daɗinsu bisa irin ayyukan ci gaba da manufofin gwamnati da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa, musamman a fannin tsaro da bunƙasa tattalin arziki. Sun yaba da yadda gwamnati ke ƙoƙarin samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da rage damuwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version