YARA SU NE GABA: ONE KANO AGENDA TA YABA WA DAN BELLO KAN TALLAFIN DA YA BA BANGAREN ILIMI
Kungiyar One Kano Agenda tana mika sakon yabo da godiya ga fitaccen matashin Kano, mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai ayyukan jin kai, Dan Bello, bisa kokarin da ya yi na gyara tare da sabunta wata makarantar firamare ta gwamnati a Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa wannan aiki ya kawo gagarumin sauyi wajen inganta yanayin koyarwa da karatu ga dalibai da malamai, tare da nuna kishin al’umma da jajircewa wajen ci gaban jama’a. A daidai lokacin da makarantu da dama na gwamnati ke fama da matsalolin gine-gine da kayan more ilimi, irin wannan gudummawa ta cancanci yabo, karfafa gwiwa da kuma goyon baya daga dukkan masu kishin kasa da ci gaban al’umma.
One Kano Agenda ta yi imanin cewa cigaban al’umma ba nauyin gwamnati kadai ba ne. Duk wani dan kasa da yake amfani da matsayinsa, tasirinsa ko dukiyarsa wajen tallafa wa ilimi, lafiya, ci gaban matasa da walwalar jama’a ya cancanci a yaba masa maimakon a sare masa gwiwa. Duk wata gudummawa mai anfani ga al’umma, ba tare da la’akari da wanda ya bayar da ita ba, ya kamata a karbe ta da kyakkyawar niyya da adalci.
Mun kuma lura da cece-kuce da suka biyo bayan launukan da aka yi amfani da su wajen fentin azuzuwan makarantar. Ya dace a fahimci cewa amfani da launuka masu kayatarwa a makarantu, musamman na yara kanana da firamare, abu ne da aka dade ana yi a Najeriya da sauran kasashen duniya domin samar da yanayi mai jan hankali da kara wa yara sha’awar karatu. Danganta kowanne irin amfani da launuka da wata akida ko manufa ta daban ba abu ne na adalci ba, kuma hakan na iya hana mutane masu niyyar taimakawa al’umma ci gaba da irin wadannan ayyuka na alheri.
Har zuwa yanzu, ba mu da wata hujja ko wata sanarwa daga Dan Bello da ke nuna yana goyon bayan ayyukan LGBTQ ko wata dabi’a da ta saba wa addini da al’adunmu. Saboda haka, yana da muhimmanci jama’a su kasance masu adalci da gaskiya wajen tattauna irin wadannan batutuwa, tare da mai da hankali kan amfanin da aikin ya haifar ga al’umma.
One Kano Agenda tana kira ga sauran masu fada a ji, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, kwararru da sauran ‘ya’yan Kano masu hali da tasiri da su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki ta hanyar zuba jari a ayyukan ci gaban al’umma, musamman a bangaren ilimi. Ko da karamin taimako ne wajen gyaran makarantu, cibiyoyin lafiya, samar da ruwa ko tallafawa matasa, yana iya haifar da babban sauyi mai anfani ga al’umma.
A matsayinmu na al’umma, ya kamata mu rika yabawa da karfafa ayyukan alheri, tare da gina dabi’ar nuna godiya ga duk masu yi wa jama’a hidima. Yawaita zarge-zarge marasa tushe, cin mutunci da suka kan masu kokarin taimakon jama’a na iya sanyaya gwiwar sauran masu niyyar bayar da gudummawa.
One Kano Agenda za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta hadin kai, ci gaba, kishin kasa, shugabanci nagari da kuma karfafa alhakin bai daya domin ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Sanya Hannu:
One Kano Agenda


