Security

Faɗan ‘Yandaba ya ɓarke a unguwar Chiranci Gabas, an tabbatar da mutuwar mutum ɗaya

aiposter 2026 04 10 073827
aiposter 2026 04 10 073827

Faɗan ‘Yandaba ya ɓarke a unguwar Chiranci Gabas, an tabbatar da mutuwar mutum ɗaya

Wani mummunan faɗa tsakanin yandaba, ya yi sanadiyyar rasa rai guda ɗaya a unguwar Chiranci Gabas, kusa da Gidan Dutse, a ƙaramar hukumar Kumbotso, Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a da misalin ƙarfe 1:30 na rana, lokacin da wasu matasa ɗauke da makamai suka fito daga yankin Layin Service da ke cikin Chiranci Gabas, suka nufi Gidan Dutse.

A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya haɗa da mazauna yankin Gidan Dutse da kuma ƙungiyar da ta shigo daga Layin Service, inda aka yi arangama .

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga zargin sata da kwacen waya, wanda ya sa mazauna yankin suka tunkari waɗanda ake zargi da shiga unguwar tasu. A yayin faɗan, an jikkata mutane da dama, yayin da aka kashe wani mai suna Bashir nan take.

Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda, sun isa wurin da abin ya faru, inda suka nemi a ba su gawar mamacin domin gudanar da bincike. Sai dai iyalan mamacin sun ƙi amincewa, inda suka yi gaggawar binne shi.

Haka kuma, shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wani daga cikin ‘yan daban ya samu munanan raunuka, kuma a halin yanzu yana karɓar kulawar likitoci a wani asibiti.

Jami’an tsaro sun tabbatar da tsaro a yankin.

A halin yanzu, ana jiran cikakken rahoto daga Hukumar ‘Yansanda domin tabbatar da cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *