YAƘI DA MIYAGUN ƘWAYOYI A KANO: NASARORIN KWAMITIN BARR. MUHYI DA SABON SALON YAƘI DA MASU SAFARAR MIYAGUN KWAYOYI
Daga: Muhammad Abubakar Suleiman
Lokacin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a ranar 22 ga Yuli, 2026, tare da ƙaddamar da Kwamitin haɗin guiwar Hukumomi da aka Ƙirƙira domin yaƙi da Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi da safararsu ba bisa Ƙa’ida ba, mutane da dama a Kano sun ɗauki matakin a matsayin wani sabon kwamiti kawai.
Sai dai bayan watanni uku, kwamitin da Lauya Muhyi Magaji Rimin Gado ke jagoranta ya zama ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankali a fannin tsaro a jihar.
An kafa kwamitin ne a matsayin dandali na haɗin guiwar hukumomi daban-daban, ciki har da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Rundunar ’Yan Sanda, Hukumar DSS, Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki, Ƙungiyar Masu Harhaɗa Magunguna, Ma’aikatar Lafiya, Sashen Yaƙi da Daba da sauran masu ruwa da tsaki.
Dr. Ibrahim Garba Muhammad ne ke riƙe da muƙamin sakataren kwamitin.
Daga Samamen Tsaro Zuwa Nasarori: An Kama Fiye da Mutum 400
Bisa bayanan da shugaban kwamitin ya gabatar, a cikin watanni biyu na farko, kwamitin ya samu nasarar kama mutane sama da 380 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, tare da tabbatar da hukuncin kotu kan sama da mutane 230.
A ranar 29 ga Satumba, lokacin da Barr. Muhyi ya gabatar da jawabi a taron karatun wata-wata na Ƙungiyar Ƙungiyoyin Sa-kai ta Kano (KANET), wanda aka gudanar a Nasarawa GRA, adadin waɗanda aka kama ya haura 400.
Lokacin da kwamitin ya gabatar da rahoton ayyukansa ga Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano a ƙarshen watan Satumba, ya bayyana cewa an samu raguwar laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi da kashi 35 cikin 100 a cikin watanni uku da suka gabata.
Kwamitin ya danganta wannan raguwar da tsaurara matakan sintiri da samamen tsaro, ƙwace miyagun ƙwayoyi da kuma tabbatar da hukuncin kotu kan sama da mutane 500 zuwa ranar 22 ga Oktoba.
Ayyukan kwamitin sun fi mayar da hankali ne kan wuraren da aka gano suna da yawan aikata laifukan da suka shafi shaye-shaye da ayyukan daba.
Wuraren sun haɗa da Race Course, Filin Idi, Filin Mahaha, Tashar Rami, Kawo, Tashar Rimi, Jakara, Madigawa, Yalwa, Sanka, Kul Kul, Dogon Nama da Kukar Bulukiya.
Daga cikin miyagun ƙwayoyin da aka ƙwato akwai Cannabis Sativa, Tramadol, Diazepam, Pentazocine, Pregabalin, Exol-5 da kuma wani nau’in ƙwayar Methamphetamine da ake ƙera wa.
A wani samame na musamman, an ƙwace capsules na Pregabalin guda 870,000 daga hannun wani kamfanin harhaɗa magunguna bisa zargin karkatar da su zuwa kasuwar haramtacciya.
Haka kuma, an ƙwato makamai da ake zargin ƙungiyoyin daba suna amfani da su, ciki har da wuƙaƙe, adduna, takubba da sanduna.
Kwamitin ya kuma samu nasarar kama wasu manyan waɗanda ake zargi. A ranar 18 ga Agusta, ya sanar da kama wani tsohon shugaban ƙaramar hukumar Rogo bisa zargin sayarwa da yi wa matasa allurar Fentanyl.
An ce an gano wanda ake zargin ne bayan wani mutum da ya kashe sama da naira miliyan biyu wajen sayen alluran ya bayyana shi a matsayin wanda ke da hannu a lamarin.
Sabon Rahoto: An Bibiyi Wanda Ake Zargi Da Daukar Nauyin Ƙungiyoyin Daba Har Zuwa Fatakwal
A wani sabon samamen da kwamitin ya gudanar, a ranar 30 ga Oktoba, ya sanar da kama wani matashi mai shekaru 27, mai suna Ishaq Lawan Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Keya, daga Yalwa da ke ƙaramar hukumar Dala.
Kwamitin ya bayyana cewa ana zargin Malam Keya da ɗaukar nauyin arangamar rikici tsakanin ƙungiyoyin daba masu hamayya a Dala, wanda ake zargin ya yi sanadin salwantar rayuka.
Rahoton ya nuna cewa wanda ake zargin ya tsere zuwa Fatakwal, Jihar Rivers, bayan da aka tsaurara matakan murƙushe ayyukan daba.
Sai dai jami’an kwamitin sun bibiyi sawunsa tare da cafke shi a wani samame da Shugaban Ayyuka na kwamitin, CSP Bashir Gwadabe, ya jagoranta.
Daga nan aka dawo da shi Kano, inda a yanzu yake hannun ‘yan sanda domin fuskantar shari’a.
Shugaban kwamitin, Barr. Muhyi Magaji, ya bayyana cewa kama wanda ake zargin a wajen jihar Kano ya nuna cewa kwamitin ba zai tsaya kan iyakokin jihar ba wajen bin diddigin waɗanda ake zargi da aikata laifuka.
Gyaran Hali Da Fasahar Zamani
Kwamitin ya bayyana cewa aikinsa bai tsaya kawai kan kama masu laifi ba, domin yana da alhakin kare yara, gyara halayen masu laifi da kuma taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.
A cewar kwamitin, an ceto yara ƙanana guda 43 da ake zargin an fallasa su ga shan miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, an tabbatar da hukuncin kotu kan wasu dillalan miyagun ƙwayoyi guda biyu, Kabiru Isa da Usman Hamisu, bisa laifukan da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi.
An kuma tura mutane kusan 125 zuwa Cibiyar Gyaran Hali ta Kano da ke Kiru domin samun kulawa da gyaran hali.
Saboda cunkoso a cibiyar Kiru, gwamnatin jihar ta samar da wata cibiyar ƙarin kulawa da gyaran hali a ƙaramar hukumar Tofa.
Kwamitin ya kuma sanya wa kansa babban buri na fitar da matasa 10,000 daga tituna domin shigar da su shirye-shiryen gyaran hali, koyon sana’o’i da kuma sake dawo da su cikin al’umma.
A ranar 21 ga Agusta, Barr. Muhyi ya ƙaddamar da ƙananan kwamitoci guda tara domin inganta tsarin yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
Ƙananan kwamitocin sun haɗa da:
1. Kwamitin Kuɗi.
2. Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a.
3. Kwamitin Wayar da Kan Al’umma.
4. Kwamitin Lasisi, Ƙididdigar Kayayyaki da Tabbatarwa.
5. Kwamitin Bin Dokoki, Bincike da Bibiyar Ayyuka ta Na’urorin Zamani.
6. Kwamitin Sa Ido da Aiwatar da Manufofi.
7. Kwamitin Leken Asiri.
8. Kwamitin Gyaran Hali da Majalisar Gargajiya.
9. Kwamitin Haɗin Gwiwar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi.
Sabon Tsari: Amfani Da Fasahar AI da tallafin hukumar NDLE
A cikin makonni biyu da suka gabata, kwamitin ya bayyana wani sabon salo na gudanar da ayyukansa.
A ranar 22 ga Oktoba, Barr. Muhyi, a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wasu kayan aikin gudanar da ayyuka ga Hukumar NDLEA ta Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandanta, Dahiru Yahaya Lawan, domin ƙarfafa ayyukan hukumar.
Ya kuma bayyana cewa Jihar Kano tana shirin amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) wajen sa ido da bin diddigin waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.
Bugu da ƙari, ana shirin samar da cibiyar gaggawa wadda za ta kasance tana amfani da fasahar sadarwa ta zamani (ICT), tare da layin waya kyauta da zai yi aiki na tsawon sa’o’i 24.
Ta wannan hanya, mazauna jihar za su iya kai rahoton duk wani motsi ko zargin da ya shafi miyagun ƙwayoyi, inda ake sa ran za a iya mayar da martani cikin mintuna 30 bayan samun rahoto.
A yayin taron karatun wata-wata na KANET mai taken, “Matsalar Miyagun Ƙwayoyi a Kano: Ƙalubale, Hanyar Magance Matsalar da Rawar da Al’umma Za Ta Taka,” Barr. Muhyi ya jaddada muhimmancin bayanan sirri daga al’umma wajen taimaka wa hukumomi.
Ya kuma yi kira da a ƙara faɗaɗa shirye-shiryen gyaran hali domin rage cunkoso a gidajen tsare mutane.
Babu Wanda Ya Fi Ƙarfin Doka
Tun daga ranar farko ta kafa kwamitin, Barr. Muhyi ya sha nanata matsayinsa na kin amincewa da duk wani katsalandan na siyasa a cikin ayyukan kwamitin.
A ranar 28 ga Yuli, ya bayyana wa manema labarai cewa:
“Babu wani ɗan siyasa da zai iya matsa mini lamba domin in saki wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Mutum ɗaya tilo da zai iya dakatar da ni shi ne Gwamna, kuma na san ba zai taɓa tsoma baki cikin aikina ba.”
Wannan matsaya, tare da samamen da ake gudanarwa bisa sahihan bayanan leƙen asiri, sun jawo yabo daga wasu ɓangarori, yayin da kuma ayyukan kwamitin ke fuskantar tambayoyi da sa ido daga al’umma.
Bayanan Rundunar ‘Yan Sandan Kano da kwamitin ya yi ishara da su sun nuna cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da aka aikata a shekarar 2025 suna da alaƙa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, umarnin zartarwa da ya haramta ayyukan ƙungiyoyin Daba ya tanadi hukuncin ɗaurin shekaru biyar a matsayin mafi ƙarancin hukunci, bisa sashe na 97A na Kundin Dokokin Laifuka na Jihar Kano.
Nasarorin Kwamiti:
Na farko, tabbatar da tsaron hanyoyin samar da magunguna, musamman hana karkatar da magungunan da kamfanonin harhaɗa magunguna ke sarrafawa zuwa kasuwar haramtacciya.
Na biyu, faɗaɗa cibiyoyin gyaran hali fiye da cibiyar Kiru domin samun damar kula da yawan mutanen da ake kamawa da kuma waɗanda ke buƙatar taimako.
Na uku, tabbatar da dorewar haɗin guiwar hukumomi ba tare da kwamitin ya zama wata hukuma mai gudanar da ayyukan tsaro daban da tsarin hukumomin da doka ta kafa ba.
A halin yanzu, a kasuwannin Filin Idi da titunan ƙaramar hukumar Dala, wasu mazauna yankunan sun bayyana cewa suna fara ganin tasirin kasancewar kwamitin a ayyukan tsaro da yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
Duk da haka, babban ƙalubalen da ke gaban kwamitin shi ne tabbatar da cewa waɗannan matakan za su zama masu ɗorewa, tare da samar da ingantaccen tsari na hana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kare rayuwar matasa da al’ummar Kano baki
