eMagazine Media Channel Letter TRCN COORDINATOR NA KANO YA BUKACI MALAMAI SU ZAMA ƘWARARRU, YA SANAR DA RANAR JARABAWAR PQE TA 2026
Letter

TRCN COORDINATOR NA KANO YA BUKACI MALAMAI SU ZAMA ƘWARARRU, YA SANAR DA RANAR JARABAWAR PQE TA 2026

images (17)

images (17)

 TRCN COORDINATOR NA KANO YA BUKACI MALAMAI SU ZAMA ƘWARARRU, YA SANAR DA RANAR JARABAWAR PQE TA 2026

Jami’in kula da Rijistar Malamai ta Ƙasa (TRCN) na Jihar Kano, Sir Hamza Muhammad, ya yi kira ga malamai da masu sha’awar shiga aikin koyarwa da su rungumi koyarwa a matsayin sana’ar ƙwararru, maimakon ɗaukar ta a matsayin aikin da mutum ya tsinci kansa a ciki ba tare da shiri ba.

Sir Hamza ya jaddada cewa, ya kamata mutum ya zaɓi koyarwa da cikakkiyar niyya, tare da kasancewa mai kishin aikin, sadaukarwa, samun horo na musamman, ƙwarewa da kuma bin ƙa’idojin da suka dace da aikin koyarwa.

Ya ce: “Kada ka zama malami bisa kuskure ko dan larurar rashin wani aikin da ka fi so. Ka tabbatar ka zama malami ta hanyar ƙwarewa da cikakken shirin sana’a.”

Ya bayyana cewa koyarwa ta wuce neman hanyar samun abin dogaro da kai, domin malamai suna da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen gina ɗabi’a, ilimi da makomar matasa da al’umma baki ɗaya.

Jami’in TRCN na Jihar Kano ya kuma tunatar da malamai muhimmancin yin rijistar ƙwararrun malamai, ci gaba da samun horo da kuma kiyaye ƙa’idojin aikin koyarwa.

TRCN TA SANAR DA RANAR JARRABAWAR PQE BATCH ‘B’ TA 2026

Sir Hamza Muhammad ya bayyana cewa, za a gudanar da Jarabawar Ƙwarewar Ƙwararrun Malamai ta Ƙasa (Professional Qualifying Examination – PQE), Rukuni na ‘B’ na shekarar 2026, a ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026.

Za a gudanar da jarabawar ne a cibiyar BMG Institute da ke kan titin Zaria Road, a Jihar Kano.

Ana shawartar dukkan waɗanda suka yi rajista domin rubuta jarabawar da su yi shiri yadda ya kamata, tare da halartar cibiyar jarabawar a kan lokaci.

Za a fara tantance masu yin jarabawar (Accreditation) da ƙarfe 8:00 na safe. Haka kuma, ana buƙatar dukkanin wadanda su ka yi rijistar da su tuntuɓi ko su ziyarci ofishin TRCN na Jihar Kano domin tabbatar da cikakkun bayanan jarabawarsu da samun dukkan muhimman bayanai kafin ranar jarabawar.

Wannan jarabawa na daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa ƙwarewa, tabbatar da inganci da kuma bunƙasa ƙwarewar malamai a Najeriya.

A ƙarshe, Sir Hamza ya ƙara ƙarfafa wa malamai guiwa da su ɗauki nauyin aikinsu da muhimmanci, yana mai cewa makomar ilimi ta dogara ne matuƙar a kan sadaukarwa, ƙwarewa da kwarewar waɗanda aka ɗora wa alhakin koyar da al’umma.

Baba Comrade

E-MAGAZINE MEDIA CHANNEL

Ilimi | Labarai | Bayanai | Wayar da Kan Al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version