eMagazine Media Channel News Tinubu ya amince da naɗin Mahmud Yakubu a jakadan Qatar, Fani-Kayode zuwa Jamus, da wasu 63.
News

Tinubu ya amince da naɗin Mahmud Yakubu a jakadan Qatar, Fani-Kayode zuwa Jamus, da wasu 63.

1771607729285

1771607729285

 Tinubu ya amince da naɗin Mahmud Yakubu a jakadan Qatar, Fani-Kayode zuwa Jamus, da wasu 63.

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura sabbin jakadun Najeriya guda 65 zuwa ƙasashe daban-daban da kuma Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

A cikin jerin akwai jakadu 31 na ma’aikatan diflomasiyya na dindindin (career ambassadors) da kuma 34 waɗanda ba ma’aikatan diflomasiyya na dindindin ba (non-career ambassadors).

Majalisar Dattawa ta tabbatar da waɗannan jakadu tun a watan Disambar da ya gabata.

 

Jerin wasu daga cikin jakadun da aka tura (Non-Career Ambassadors)

Sanata Grace Bent – Lome, Togo

Sanata Ita Enang – Afirka ta Kudu

Victor Ikpeazu – Spain

Nkechi Linda Ufochukwu – Tel-Aviv, Isra’ila

Mahmud Yakubu – Qatar

Paul Oga Adikwu – Vatican City

Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas – Philippines

Reno Omokri – Mexico

Abasi Braimah – Hungary

Angela Adebayo – Portugal

Olumilua Oluwayimika Ayotunwa – Japan

Ifeanyi Ugwuanyi – Greece

Chioma Priscilla Ohakim – Poland

Aminu Dalhatu – Birtaniya (United Kingdom)

Abdulrahman Dambazau – China

Tasiu Musa Maigari – Gambia

Olufemi Pedro – Australia

Muhammed Ubandoma Aliyu – Argentina

Lateef Kayode Are – Amurka

Joseph Sola Iji – Rasha

Jimoh Ibrahim – Wakilin dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya

Femi Fani-Kayode – Jamus

Isaak Folorunso Adewole – Canada

Fatima Florence Ajimobi – Austria

Lola Akande – Sweden

Ayodele Oke – Faransa

Yakubu N. Gambo – Saudiyya

Nora Ladi Daduut – Koriya ta Kudu

Joe Okocha – Ireland

Kulu Haruna Abubakar – Tunisia

Jerry Samuel Manwe – Trinidad and Tobago

Jakadu na ma’aikatan diflomasiyya (Career Ambassadors)

Wasu daga cikin waɗanda aka tura sun haɗa da:

Nwabiola Ezenwa Chukwumeka – Côte d’Ivoire

Besto Maimuna Ibrahim – Nijar

Mohammed Mahmud Lele – Algeria

Ahmed Mohammed Monguno – Masar

Jane Adams Michael – Jamaica

Alexandra Clark-Omeru – Zambia

Geoffrey Lioma David – Mali

Yvonne Ehinosen Odumah – Equatorial Guinea

Segun Ige – Lebanon

Ruben Abimbola Samuel – Italy

Ogechukwu Kingsley Onaga – Mozambique

Umar Magaji – DR Congo

Muhammad Saidu Dahiru – India

Abdussalam Habu Zayyad – Senegal

Shehu Ilu Barde – Ghana

Aminu Nasir – Ethiopia

Abubakar Musa – Chadi

Mohammed Idris Haidara – Netherlands

Bako Adamu Umar – Morocco

Olatunji Ahmed Sulu Gambari – Malaysia

Romata Mohammed Omobolanle – Tanzania

John Shamah – Botswana

Hamza Mohammed Salau – Iran

Ibrahim Danlami – Kenya

Adeola Mopelola Ibrahim – Benin

Adebayo Emmanuel Ayeni – Belgium

Wahab Adekola Akande – Switzerland

Esther Arewa – Namibia

Joseph John Gergadi – Gabon

Luther Ayo-Kalata – Sierra Leone

Danladi Yakubu Nyaku – Sudan

Bello Dogon-Daji Haliru – Thailand

Najeriya ta riga ta samu amincewar gwamnatin Birtaniya ga sabon Babban Jakadan Najeriya da aka naɗa, wato Ambasada Aminu Dalhatu. Haka kuma, Faransa ta amince da naɗin Ambasada Ayo Oke.

Ma’aikatar ta kuma tura sunayen sauran jakadun zuwa ƙasashen da za su yi aiki domin neman amincewar su, kamar yadda dokokin diflomasiyya suka tanada.

Shugaba Tinubu ya umarci Ma’aikatar Harkokin Waje da ta gaggauta fara shirin horaswa ga sabbin jakadun kafin su fara aiki a ƙasashen da aka tura su.

Sanarwar ta fito ne daga Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version