Politics

Sakatarorin Ilimi Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sun Yaba da Gyare-gyaren Ilimi

IMG 20260212 WA0004
IMG 20260212 WA0004

Sakatarorin Ilimi Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sun Yaba da Gyare-gyaren Ilimi

Ƙungiyar Sakatarorin Ilimi na Kananan Hukumomi 44 na Jahar Kano ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta kuma bayyana gamsuwarta da jajircewar gwamnati wajen farfaɗo da bangaren ilimi.

Ƙungiyar ta bayyana wannan matsaya ne yayin wata ziyarar nuna goyon baya da suka kai wa Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda ya karɓi tawagar a madadin Maigirma Gwamnan Jahar Kano.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Nura Suleiman, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce Sakataren Ilimi sun ga dacewar su mara wa wannan gwamnati baya duba da irin fifikon da ta bai wa ilimi, wanda ya bayyana a matsayin abin a yaba. Ya ƙara da cewa, yawan kasafin kuɗin da aka ware wa bangaren ilimi na nuna ƙwararan matakan Gwamna wajen sake gina wa da ƙarfafa tsarin ilimi a Jahar Kano.

Alhaji Nura ya kuma bayyana cewa mambobin ƙungiyar sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da rabon kayan makaranta kyauta da littattafan karatu da gwamnatin jaha ta samar, inda ya bayyana shirin a matsayin gagarumin shiri wanda ya kawo sauyi maikyau a makarantun dske faɗin jahar Kano.

Ƙungiyar ta kuma yaba wa gwamnati kan warware matsalar jinkirin ƙarin girma (promotion) na malamai da ta daɗe tana addabar su, inda ta bayyana hakan a matsayin babban abin ƙarfafa guiwa da ya ƙara himma, ƙwazo da sadaukarwar malamai wajen aikinsu.

Sakatarorin sun kuma tabbatar wa da Kwamishinan cikakken goyon bayansu ga tafiyar Gwamna Abba. Haka zalika Sakatarorin na Ilimi sun yi alƙawarin ci gaba da wayar da kan jama’a a matakin tushe domin tabbatar da nasarar manufofin ci gaba da mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A nasa jawabin, Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma da sauyin tattalin arziki. Ya jaddada cewa ci gaba da zuba jari da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi a bangaren ilimi wata dabara ce da za ta tabbatar da kyakkyawar makoma ga al’ummar Jahar Kano.

Kwamishinan ya yaba da rawar da Sakatarorin Ilimi ke takawa wajen aiwatar da manufofin gwamnati a matakin ƙasa, inda ya ce jajircewarsu da kwarewarsu na da matuƙar muhimmanci ga nasarar gyare-gyaren ilimi da ake gudanarwa.

Ya bayyana cewa ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗin shekarar 2025 da kuma kashi 31 cikin 100 na kasafin 2026 ga ilimi na nuna ƙudirin Gwamna na sake farfaɗo da bangaren domin samun ci gaba mai ɗorewa da nagarta.

Hon. Waiya ya nuna matuƙar godiya ga Ƙungiyar bisa goyon baya da suke bai wa gwamnatin, musamman ga ajandar “Kano First”, wadda ya ce an tsara ta ne domin ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, ci gaba mai ɗorewa da kishin jihar Kano.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *