News

REGISTER TIN NUMBER BA DOLE BA NE , MATUKAR KANA DA LAMBAR NIN KO TA CAC

images (15)
images (15)

A ranar Talata 23/12/2025 wakilin E-Magazine Media Channel Baba Comrade ya yi tattaki har zuwa hukumar FIRS ta Nigeria dake jahar Kano a inda suka tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar rejistar haraji ta TIN da ake ta yamitsa hazo musamman a tsakanin ma’aikata.

Ga irin hirar da mu ka yi da jami’an FIRS:

Ga Muhimman Bayanai da su ka yi wa wakilanmu:

1. Wajibi ga Masu Biyan Haraji:* Daga 1 ga Janairu, 2026, duk wani mutum ko kamfani da ke samun kuɗi (wato “taxable person”) dole ne ya mallaki TIN kafin bude ko gudanar da asusun banki, yin hulɗar inshora ko harkokin kasuwar hannun jari, da kuma shiga kwangilolin gwamnati.

2. Ba Buƙatar Samun Sabuwar Katin TIN: Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta bayyana mana cewa ba sai mutum ya je ya karɓi sabuwar katin lambar TIN ba. Sabon tsarin yana hade da manyan bayanan kasa da suka riga dama suna aiki, ma’ana –

Mutum ɗaya zai yi amfani da Lambar Shaidar Ƙasa (NIN) a matsayin TIN ɗinsa.

– Kamfanoni kuma za su yi amfani da Lambar Rajistar CAC a matsayin TIN ɗinsu.

3. Hada Kai Ta Atomatik: Da zarar mutum ya bayar da NIN dinsa yayin buɗe asusun banki ko sabunta bayanan KYC, tsarin zai haɗa shi da bayanan harajinsa kai tsaye ba tare da yin wata ƙarin nema ba.

4. Wanda Ba Ya Ciki: Wadanda ba su da haraji da ake buƙata su biya, irin su ɗalibai da masu dogaro da wasu, ba su cikin waɗanda dokar ta shafa.

5. Hukunci Ga Wanda Bai yi Ba: Idan kamfani ko mutum mai hakkin biyan haraji bai samu ko amfani da TIN ba bayan wa’adin, zai iya fuskantar hukunci, ciki har da toshe asusun banki.

6. Manufa: Wannan gyaran zai sauƙaƙa bin doka wajen biyan haraji, ya faɗaɗa hanyar tara haraji a ƙasa, ya inganta samun kuɗaɗen shiga, da tabbatar da gaskiya a harkokin kuɗi ta hanyar rufe hanyoyin kaucewa biyan haraji.

images (15)

A takaice dai idan mutum yana da lambar NIN shi ke nan , ba sai ya yi wata sabuwar lambar haraji ba.

Ma’aikata sai ku kwantar da hankalinku tunda kowa yana da NIN .

Baba Comrade, E-Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *