News Uncategorized

NUT TA BA WA WAKILANTA HORO AKAN SOCIAL MEDIA

IMG 20260117 WA0022
IMG 20260117 WA0022

Ƙungiyar NUT ta ba wa wakilanta horo na musamman akan yadda ake amfani da kafafan sadarwa na online

Ƙungiyar Malaman makaranta ta Nigeria reshen Jahar Kano ta ba wa wakilanta horo na musamman akan sanin ƙa’idoji da dokokin amfani da kafafan sadarwa na zamani a ranar Asabar 17/1/2026 a rufaffen ɗakin taro na ƙungiyar bisa jagorancin Comrade Umar Tijjani Isa(Managing Editor).

IMG 20260117 WA0013

Comrade Umar Tijjani Isa ya yi jawabin dalilan da yasa aka bada wannan horo na musamman, a inda ya ke cewa, “wannan bita an yi tane domin samar da hanyoyin da suka dace wajan bayyana wa malaman makaranta ire-iren ayyukan da ƙungiya ta ke yi wa malaman makaranta.” Isah ya ƙara da cewa, “a rashin bayyana wa malaman makaranta halin da ƙungiya ke ciki ne ya sa wasu malaman su ke ganin ƙungiyar ba ta yin abun da suka dace na taimaka wa malaman.”

IMG 20260117 WA0027

Comrade Umar a madadin shugaban ƙungiyar NUT na jahar Kano ya ƙara da cewa, NUT na sauke nauyin malaman makaranta tare da taimaka musu yadda ya kamata kuma bisa doka.

IMG 20260117 WA0029

Ƙungiyar ta NUT ta ja hankalin malaman makaranta da su yi watsi da duk wata propaganda da ake yi akan ƙungiyar na ɓatanci a kafafen sada zumunta. Domin kungiyar tana aiki tukuru cikin lumana domin warware matsalolin malaman ta hanyar da ta dace.

IMG 20260117 WA0024

IMG 20260117 WA0026

IMG 20260117 WA0023

Baba Comrade, E-magazine

17/1/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *