News

NUT: COMRADE HAMBALI YA ZAMA NATIONAL 1st VICE PRESIDENT

IMG 20260215 WA0010
IMG 20260215 WA0010

COMRADE MUHAMMAD ABUBAKAR HAMBALI YA ZAMA MATAIMAKIN SHUGABAN ƘUNGIYAR MALAMAN MAKARANTA TA NIGERIA (NUT)

Ƙungiyar Malaman makaranta ta Nigeria NUT ta ƙara wa Comrade Muhammad Hambali Abubakar girma daga matsayin Mataimaki na biyu ( 2nd Vice President) zuwa matsayin mataimaki na ɗaya (1st VICE PRESIDENT). A inda sauran shugabannin suma su ka matsa zuwa mataki na gaba(adjustment according to the seniority rank) bisa dokar da kundin tsarin mulkin kungiyar ya tanada.

IMG 20260215 WA0009

Shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen Jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim  Garko ya mika sakon godiya ga shugabancin kungiyar NUT ta ƙasa bisa daga likafar Hambali da aka yi daga matakin Second Vice President zuwa matakin First Vice President na NUT. Garko ya isar da wannan godiyar ce a madadin dukkanin malaman makaranta na jahar Kano tare da gode wa Allah SWT. Garko ya kuma taya Comrade Sani Haladu Gwarzo murna bisa ƙarin girma da ya samu zuwa matakin Director Schools Service a hukumar KSSSSMB. Haka zalika ya taya Comrade Hadiza Yari ita ma murnar zama Deputy Director na Model Schools.

Comrade Muhammad Hambali Abubakar a nasa jawabin ya ce, hakika ya ji daɗin da irin karamci da goyon baya da dukkanin malaman makaranta na jahar Kano su ke bashi, musamman ma SWEC Members. Hambali ya kuma ja kunnen shugabannin kungiyar na rassan ƙananan hukumomin jahar Kano 44 da su yi kokari su zauna lafiya da kuma taimakawa malaman makaranta.

Garko ya kuma shaida wa malaman makaranta cewa, Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince tare da bada umarni da a shigarwa dukkanin malaman makaranta kudadensu na Promotion ga wadanda suka cancanta. Garko ya ja kunnen malaman makaranta da su ke zuwa wajan aiki tare da yin aikin da ya dace.

Hambali ya godewa Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf akan taimaka wa da ya ke yi wajan shigar wa da malaman makaranta kudadensu na Promotion akan lokaci.

Baba Comrade, E-magazine

15/2/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *