Nadin Shugabannin Ilimi Bakwai a Matsayin Sakatarorin Dindindin da Gwamna Yusuf Ya Yi abu ne da ya ƙara ɗaga darajar ilimi a Duniya-Ja’e
Daga Kwamared Jae
Nadin Sakatarorin Dindindin guda bakwai daga Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSSMB) da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi, ya samu karɓuwa sosai tare da kasancewa wani babban tarihi da ke nuna muhimmancin malamai da masu gudanar da harkokin ilimi wajen jagoranci da gudanar da gwamnati. Haka ya ƙara ɗago da darajar ilimi da malamai a fadin Duniya.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Malam Nura Abba Dandago, Hajiya Hauwa Nuhu Wali, Hajiya Uwani Ahmad Balarabe, Hajiya Rabi Inuwa Hussain, Hajiya Hannatu Ado Gwaram, Malam Aliyu Tsoho da Dakta Sani Gwarzo. Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun bayyana nadin nasu a matsayin girmamawa ga ƙwarewa, nagarta, gaskiya da kuma shekaru masu yawa na hidima ga al’umma.
Masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi sun bayyana cewa wannan mataki ya sake farfaɗo da martabar malamai, domin ya nuna cewa sadaukarwa a koyarwa, ƙwarewa a shugabancin makarantu da hidimar gwamnati har yanzu su ne hanyoyin kaiwa ga manyan mukaman shugabanci.
Sabbin Sakatarorin Dindindin suna da gogewa mai ɗimbin yawa wajen gudanar da harkokin ilimi, aiwatar da manufofi, kula da ma’aikata da bunƙasa cibiyoyin ilimi. Ana sa ran wannan ƙwarewa za ta ƙarfafa aiwatar da manufofin gwamnati tare da inganta tsarin gudanar da harkokin gwamnati a Jihar Kano.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka yaba da nadin shi ne Abubakar, Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Ƙididdiga a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano. Ya bayyana nadin a matsayin wani babban ci gaba ga sana’ar koyarwa da kuma abin alfahari ga malamai a faɗin jihar.
A cewarsa, kasancewarsa ya yi aiki tare da yawancin waɗanda aka naɗa tun daga matsayin malami, shugaban makaranta da kuma Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Nijeriya (ANCOPSS), ya ba shi damar shaida ƙwarewarsu, tawali’unsu da kuma jajircewarsu wajen ci gaban ilimi a Kano.
Ya yi yabo na musamman ga Hajiya Uwani Ahmad Balarabe da Hajiya Hauwa Nuhu Wali, inda ya bayyana su a matsayin fitattun shugabannin ilimi da suka gina rayuwarsu ta aiki bisa sadaukarwa, hangen nesa da kuma hidima mai inganci.
Ya bayyana cewa Hajiya Uwani Ahmad Balarabe ta shafe kusan shekaru talatin tana hidima, inda ta fara a matsayin malamar aji kafin ta zama Babbar Malama (Senior Mistress), Mataimakiyar Shugabar Makaranta, Shugabar Makaranta, sannan Babbar Daraktar Kwalejin ‘Yan Mata ta Gwamnati, Kano. A matsayinta na Shugabar ANCOPSS ta Jihar Kano, ta jagoranci shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar shugabannin makarantu, ta ƙarfafa haɗin guiwa tsakanin cibiyoyin ilimi tare da wakiltar Kano cikin kwarewa a shirye-shiryen ilimi na ƙasa da tarurruka daban-daban.
Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancinta ne Jihar Kano ta karɓi bakuncin manyan shirye-shiryen Mandatory Continuing Professional Training (MCPT), wanda dubban shugabannin makarantu suka amfana da su, lamarin da ya inganta ƙwarewar masu gudanar da harkokin ilimi a jihar.
Haka kuma ya bayyana Hajiya Hauwa Nuhu Wali a matsayin gogaggen shugabar ilimi mai fiye da shekaru 31 tana hidima. Ta fara daga koyarwa kafin ta zama Shugabar Makaranta, Mataimakiyar Darakta da Babbar Daraktar Kwalejin ‘Yan Mata ta Gwamnati Kano da ta Dala, inda ta nuna ƙwarewa ta musamman wajen gudanar da harkokin ilimi.
Ya kuma yabawa irin gudummawar da ta bayar a ANCOPSS, inda ta yi aiki a matsayin Ex-Officio cikin aminci da ƙwarewa, abin da ya sa ta samu girmamawa saboda nutsuwarta, hikimarta da jajircewarta wajen tabbatar da ci gaban ƙungiyar.
A cewarsa, Hajiya Hauwa ta bullo da shirye-shiryen haɓaka ƙwarewar malamai, ta ƙarfafa haɗin guiwa tsakanin makarantu da al’umma, ta inganta gaskiya a tafiyar da makarantu tare da jagorantar matasa malamai da shugabannin ilimi. Ya ce lambobin yabo da karramawa da ta samu daga Ma’aikatar Ilimi, SERVICOM, ANCOPSS, British Council da sauran ƙungiyoyi sun tabbatar da rayuwar aiki mai cike da ƙwarewa da nagarta.
Malama Hannatu Ado Gwaram ta zama ɗaya daga cikin Principals na makarantu da su ka yi fice wajen samar da ci gaban ilimi a jahar Kano.
Ya jaddada cewa wannan nadin ya nuna a fili cewa malamai suna da dukkan halayen shugabanci, ƙwarewar gudanarwa da hangen nesa da ake buƙata domin gudanar da manyan muƙaman gwamnati.
Ya ce, “Shugabannin makarantu na kula da manyan cibiyoyi, suna tafiyar da kasafin kuɗi, suna jagorantar ɗaruruwan ma’aikata, suna aiwatar da manufofin gwamnati, suna sasanta rikice-rikice tare da haɗa kai da al’umma. Waɗannan nauyin aiki suna shirya su sosai domin manyan mukaman jagoranci a aikin gwamnati.”
Ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya gano ɗimbin ƙwararrun ma’aikata da ke cikin tsarin ilimi, yana mai bayyana nadin a matsayin babban nuna amincewa da malamai da masu gudanar da harkokin ilimi.
Ya bayyana kwarin guiwar cewa sabbin Sakatarorin Dindindin guda bakwai za su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar gaskiya, kirkire-kirkire, adalci da shugabanci mai kawo sauyi.
Yayin da yake taya su murna, Abubakar ya ce wannan nasara ba ta su kaɗai ba ce, nasara ce ga daukacin malaman Jihar Kano da kuma sana’ar koyarwa baki ɗaya.
Ya kuma nuna tabbacin cewa yadda za su gudanar da ayyukansu zai ƙara tabbatar wa jama’a cewa malamai suna da cikakkiyar ƙwarewa wajen jagoranci, tsara manufofi da gudanar da manyan ayyukan gwamnati.
Masu sa ido kan harkokin gwamnati sun bayyana cewa wannan nadi ya sake tabbatar da gaskiyar cewa gogaggun malamai da shugabannin makarantu suna da ilimi, ladabi, ƙwarewa da nagartar shugabanci da ake buƙata domin bayar da gudummawa mai amfani ga ci gaban gwamnati da bunƙasar al’umma.
A ƙarshe, an bayyana wannan nadi a matsayin wani muhimmin tarihi a aikin gwamnati na Jihar Kano, inda masu ruwa da tsaki a fannin ilimi suka ce wannan mataki ya sake tabbatar da cewa idan aka bai wa malamai damar jagoranci, al’umma baki ɗaya ce ke amfana.
