Education Uncategorized

MA’AIKATAR ILIMI TA JIHAR KANO KARKASHIN JAGORANCIN MAL YUSIF KABIR TANA YI WA MA’AIKATA YAN BESDA(COHORT IV) SU KIMANIN 4315 HORO NA MUSAMMAN A FADIN JAHAR KANO

aiposter 2026 01 05 043756
aiposter 2026 01 05 043756
  • MA’AIKATAR ILIMI TA JIHAR KANO KARKASHIN JAGORANCIN MAL YUSIF KABIR TANA YI WA MA’AIKATA YAN BESDA(COHORT IV) SU KIMANIN 4315 HORO NA MUSAMMAN A FADIN JAHAR KANO

January 05, 2026

Ayau 5/1/2026 Hukumar Ilimi Ta Jihar Kano Karkashin Jagorancin Mal Kabir Yusif ta fara ba wa malaman BESDA Cohort 4 su 4315 Horo na musamman Wanda Ake yi Ayau A makarantar primary dake Dukawuya .

Hukumar Ilimin baidaya ta jahar Kano ta samar da santocin ba wa malaman BESDA da aka maida su ma’aikata na dundundun a fadin jahar Kano a inda ake ba wa malaman da suka futo daga hukumomin Ilimi wadanda suka hada da Karamar hukumar Kumbotso LGEA, Gwale LGEA da Karamar hukumar Madobi a makarantar primary ta Dukawuya Girls Science Project dake Gwale.

Megirma shugaban sashen Ilimi na karamar Hukumar kumbotso Mal Aminu Abdulahi ya yi wa Jamiar yada labarai takaramar Hukumar kumbotso akan muhimmancin Harkar koyo da koyarwa Wanda megirma eng Abba Kabir Yusif ya dauki ragamar Horarwar tare da Hadin guiwa da kungiyar NUT da plane ta Jihar Kano.

Ga irin tattaunawar da muka yi da wasu daga cikin malaman da ake ba wa bita a halin yanzu. Ga abinda Malaman Ibrahim Uba Abdurrahman ya ke cewa,” Hakika wannan horo da ake bamu yana da mahimmanci, saboda ana tuna mana mahimman abubuwa da aka koya mana a makaranta wadanda za su sake zaburar da mu a harkar koyarwa. Sannan kuma ina ba wa malaman BESDA shawara da mu yi aiki da abun da muka koya a wannan bita.”

Khadija Ahmad musa

Jamiar yada labarai TA sashen Ilimi Dake kumbotso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *