LABARAI

INEC TA FARA KARƁAR APPLICATION NA NEMAN AYYUKAN MA’AIKATAN WUCIN GADI NA ZAƁEN 2027

images (13)
images (13)

INEC TA FARA KARƁAR APPLICATION NA NEMAN AYYUKAN MA’AIKATAN WUCIN GADI NA ZAƁEN 2027

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta buɗe tashar yanar gizon hukumarta domin fara karɓar aikace-aikacen ’yan Najeriya da ke neman ayyukan wucin gadi a lokacin babban zaɓen shekarar 2027.

Za a rufe karɓar aikace-aikacen da ƙarfe 12:00 na dare ranar 18 ga Nuwamba, 2026.

Daga cikin mukaman da ake neman ma’aikata akwai Supervisory Presiding Officers, Registration Area Centre Managers, ma’aikatan Tallafin Fasaha (Technical Support), Presiding Officers da Assistant Presiding Officers.

Masu neman aikin da suka cancanta, ciki har da mambobin NYSC, ɗaliban manyan makarantu da ma’aikatan gwamnati a wasu daga cikin mukaman, dole ne su cika sharuddan da aka gindaya ga kowane matsayi.

Haka kuma, galibin masu neman aikin ana buƙatar su kasance mazauna jihar da suka zaɓa, sannan ba su kasance mambobin wata jam’iyyar siyasa ba, kuma ba su kasance masu bayyana goyon baya ga kowace jam’iyyar siyasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *