Gwamnan jahar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf Ya Jaddada Kudurin Gwamnatinsa Ga Manufar One Kano Agenda, Ya Yi Kiran Haɗin Kai da Aiki Tare.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na bin tafarkin One Kano Agenda, inda ya jaddada cewa haɗin kai da ɗaukar nauyin juna na da matuƙar muhimmanci wajen dawo da martabar jihar Kano da kuma inganta ci gaba mai ɗorewa.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ba da cikakken goyon baya ga wannan tsari, yana me cewa lokaci ya yi da al’ummar Kano za su dunƙule waje ɗaya. Ya bukaci jama’ar jihar da su tuna da matsayin Kano shekaru arba’in zuwa hamsin da suka wuce, lokacin da take jagora a fannoni kamar ilimi, kasuwanci, noma, cigaban matasa, ɗabi’un al’adu da kuma karfaffun masarautu da ake koyi da su a faɗin ƙasar nan.
A cewarsa, dawo da wannan matsayi na Kano na bukatar ƙoƙari na musamman da haɗin kai a tsakanin al’ummomi daga bangarori daban-daban na siyasa, zamantakewa da al’adu. Ya ƙara da cewa haɗin kai zai taimaka wajen shawo kan manyan ƙalubale kamar yawan shan miyagun ƙwayoyi, tare da samar da zaman lafiya da ci gaba na bai daya a cikin jihar.
SSG ya bayyana cewa gwamnatin NNPP da ke kan mulki ta cika kusan kashi 85 cikin 100 na alkawuran da ta ɗauka yayin kamfen, yana mai tabbatar da cewa kashi 15 na saura za a kammala su. Ya kuma bayyana cewa kafin shigowar lokacin zaɓe na shekarar 2027, gwamnatin za ta sabunta da kuma faɗaɗa alkawuranta na ci gaba domin ganin an samu Kano mai armashi da walwala.
A baya, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga al’umma da su rungumi sadaukarwa da jajircewa wajen aikin gina Jihar Kano tare. Ya jaddada irin tallafin da gwamnatin ke bai wa tsofaffin ma’aikata da ‘yan fansho da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimtawa jihar, tare da bayyana shirin gwamnatin na miƙa irin wannan taimako ga tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da suka yi aiki daga shekarar 2014 zuwa 2023.
Taron tattaunawar da aka shirya da masu ruwa da tsaki ya samu halartar kungiyoyin matasa, kungiyoyin farar hula da sauran ƙungiyoyi, inda aka mayar da hankali kan ci gaban Jihar Kano da kuma matakan da za a ɗauka domin magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da jihar ke fuskanta.